Majalisar Dokokin Kano Ta Fusata bayan Gano Abin da ake Yi a Gidajen da Kwankwaso Ya Gina
- Majalisar Dokokin Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar ta umarci masu kangwaye su kammala gine-ginen ko su sayar
- Dan Majalisa, Usman Abubakar Tasi'u, ya ce gine-ginen kangwaye da ba a kammala ba sun zama wuraren bata tarbiyya
- Shi ma Dan Majalisar Madobi, Sulaiman Mukhtar Ishaq, ya yi Allah wadai da rashin kammala gine-ginen a sassan jihar
- Majalisar Dokokin Kano ta kafa kwamiti da zai binciko halin da kangwaye suke ciki a jihar domin daukar matakin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnati ta umarci masu kangwaye a jihar da su gine shi ko su sayar domin inganta tsaro.
Hakan ya biyo bayan kudurin da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kiru Usman Abubakar Tasi'u ya gabatar a zauren majalisar.

Asali: Facebook
Premier Radio ta wallafa a shafinta na Facebook cewa Kiru ya ce da yawa daga cikin kangwaye da gidajen da ba'a karasa ba a jihar nan sun zama wuraren bata tarbiyya da barazanar tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa lokaci ya yi da za a dauki matakin da ya dace a a kan gine-ginen da ba a kammala su na domin kara inganta zaman lafiya da ake mora a yanzu.
Majalisa ta fusata a kan watsi da gine-gine
Daily Post ta wallafa cewa a zaman majalisar dokokin Kano da ya gudana a ranar Talata, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Madobi, Sulaiman Mukhtar Ishaq ya magantu.
Ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa gine-ginen da ba a kammala ba, ciki har da Amana, Bandirawo da Kwankwasiyya su na kawo barazana ga tarbiyyar mazauna Kano.
Ya ce:
"Wannan magana ce mai muhimmancin gaske, duba da irin yanayi na matsalolin zamantakewar mu,wanda kangwayen nan su ke jawo mana."

Kara karanta wannan
Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano
"Bayan matsalar rashin tsaro da ya yi magana a kai, ana bata matasanmu da mata.
"Hatta sababbin garuruwan nan wanda tsohuwar gwamnatin jagora, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi na Kwankwasiyya da Amana da Bandirawo, su ma akwai irin wannan matsalolin."
Kangwayen Kano: Majalisar dokoki za ta dauki mataki
Majalisar dokokin Kano ta kafa kwamiti tare da dora masa alhakin binciko halin da kangwaye suke ciki a Kano domin mika wa ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Ana sa ran za a yi amfani da rahoton wajen tilasta wa masu gidaje da sauran kadarorin da aka dakatar da gina wa su kammala aiki ko a sayar ga wanda za su yi aikin.
Majalisar ta kuma jaddada kudurin tabbatar da an kawo karshen matsalolin shaye-shaye, kwacen waya da fadan daba da ya zama karfen kafa, musamman a cikin birni.
Majalisa na son a samar da hukumar tsaro
A wani labarin, mun wallafa cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta yi karatu na biyu kan kudirin kafa Hukumar Tsaro, wanda zai rika karbar umarni daga gwamna.
Hukumar za ta taimaka wajen kara karfin jami’an tsaro, tare da ba su ikon daukar makamai da kame wadanda ake zargi da laifi, domin kamar ayyukan bata gari a Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng