Jirgin Max Air da Ya Tashi daga Legas zuwa Kano Ya Yi Hatsari, An Samu Karin Bayani

Jirgin Max Air da Ya Tashi daga Legas zuwa Kano Ya Yi Hatsari, An Samu Karin Bayani

  • Wani jirgin Max Air dauke da fasinjoji 53 da ma'aikata shida da ya taso daga Legas zuwa jihar Kano ya yi hatsari a daren ranar Talata
  • An rahoto cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 10:19 na dare a daidai lokacin da jirgin ke sauka a filin sauka da tashi na Malam Aminu Kano
  • Kamfanin Max Air ya fito ya yi karin bayani game da wannan hatsarin tare da bayyana halin da fasinjoji da ma'aikata ke ciki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Wani jirgin kamfanin Max Air mai lamba 5N-MBD, B733 ya yi hadari a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a daren ranar Talata.

Jirgin yana dauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida kuma yana dawowa daga jihar Legas ne lokacin da hadarin ya faru.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Fasinja ya yi magana yayin da jirgin Max Air ya yi hatsari a Kano
Jirgin Max Air dauke da mutane sama da 55 ya yi hatsari a filin jirgin Kano. Hoto: @MaxAirLtd
Asali: Facebook

Jirgin Max Air ya yi hatsari a Kano

Wani fasinja ya tabbatar da faruwar hadarin ga jaridar Daily Nigerian inda ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare.

"Daidai lokacin da tayar ta taba kasa, sai ta kama da wuta, hayaki ya turnuke a cikin jirgin wanda ya sa dole muka fita ta kofar fitar gaggawa
''Yayin da muke fitowa daga jirgin, wasu 'yan kashe gobara sun riga sun fara watsawa jirgin ruwa domin kashe wutar."

- A cewar fasinjan.

Kamfanin Max Air ya yi karin bayani

Da yake zantawa da jaridar SolaceBase, Manajan Max Air reshen jihar Kano, Malam Bello Ramalan, ya ce ba a samu asarar rai ko jin rauni ba.

Kara karanta wannan

Wata tankar man fetur ta sake fashewa a jihar Neja, ana fargabar mutane sun mutu

"Ina bada hakuri bisa matsalar da ta faru, kuma muna godiya ga Allah bisa tseratar da fasinjojin da ya yi. Ni lafiyar fasinjoji ce a gabana.
"Dangane da bin dokokin saukar jiki, kamfaninmu ya bi ka'idojin da suka dace na yin saukar gaggawa, wanda Allah ya sa abin ya zo da sauki.
"Ka’idojin sun hada da fitar da fasinjoji cikin gaggawa, killace matuka jirgin da kuma hada kai da hukumomin bincike."

- Malam Bello Ramalan.

Max Air ya fadi abin da bincike ya nuna

Kamfanin Max Air ya ce yana aiki tare da hukumar binciken hadurran jiragen sama (AIB) da AED domin bincike kan dalilin hadarin jirgin.

Malam Ramalan ya ce:

"Bincike na farko ya nuna cewa matsalar tayar jirgin ce ta haddasa hadarin.
"Max Air na daukar tsaro da muhimmanci kuma muna daukar matakan kare lafiyar fasinjojinmu da ma’aikatanmu."
"Ina sake bada hakuri bisa matsalar da aka samu, za mu tabbatar da cewa duk kayayyakin fasinjoji sun dawo gare su cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

NAHCON ta zabi jiragen jigilar alhazan 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar jin dadin alhazai ta kasa, NAHCON ta zabi kamfanin Max Air da wasu kamfanoni domin jigilar maniyyata aikin Hajjin 2025.

A cewar hukumar NAHCON, fadar shugaban kasa ta zabi kamfanonin jirage huɗu da za su yi jigilar alhazai, ciki har da Air Peace, Fly-Nas, Max Air da UMZA.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel