Jami'an DSS Sun Cafke Mai Safarar Makamai daga Nijar zuwa Najeriya
- Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar cafke wani tantirin mai safarar makamai a cikin jihar Zamfara
- Mai safarar makaman wanda ya tsero daga Jamhuriyar Nijar ya shiga hannu ne bayan an samu bayanan sirri a kan ayyukansa
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yabawa jami'an tsaron kan wannan nasarar da suka samu ta cafke wanda ake zargin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi nasarar kama wani wanda ake zargi da safarar makamai a jihar Zamfara.
Jami'an na DSS sun cafke wanda ake zargin ne bayan ya tsere daga Jamhuriyar Nijar zuwa jihar Zamfara.
DSS ta cafke mai safarar makamai
Tashar Channels tv ta rahoto cewa an gabatar da wanda ake zargin ga gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau a yammacin ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake magana da manema labarai bayan gabatarwar, Gwamna Dauda Lawal ya yabawa hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro kan ƙwazo da ƙwarewarsu wajen bin sawun wanda ake zargin har zuwa kama shi.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin jama'a su ba da haɗin gwiwa wajen yaƙi da ayyukan laifi.
Ya bayyana cewa ba za a iya magance matsalar rashin tsaro ba sai an samu cikakken haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da al’umma.
Gwamna Lawal ya bayyana cewa wanda ake zargin an daɗe ana sanya masa idanu kafin kama shi, inda aka bi sawunsa daga Jamhuriyar Nijar zuwa jihar Zamfara.
Wannan ya nuna yadda haɗin gwiwa ta ba da bayanan sirri tsakanin hukumomi ya taka muhimmiyar rawa wajen cafke wanda ake zargin.
Samamen da ya kai ga kama wanda ake zargin ya haɗa da dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji.
An samu nasarar samamen ne bisa samun bayanan sirri game da masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya.
An ƙwato makamai a Zamfara
An samu makamai masu yawa daga hannun wanda ake zargin, wanda suka haɗa da, bindigogi biyu na PKT, AK-47 guda tara, jigidar bindiga guda 13, harsasai guda 171 na musamman masu kaurin 7.62mm da harsasai guda tara na PKT.
Gwamna Lawal ya ƙara da cewa gwamnati tana yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaro a Zamfara, tare da tabbatariwa al’ummar jihar cewa za a ci gaba da kai hare-hare kan masu aikata laifi da masu kawo rashin zaman lafiya.
Ya yi kira ga jama’a su bayar da hadin kai ta hanyar samar da bayanai ga hukumomin tsaro, domin a kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro a jihar da Najeriya baki ɗaya.
Jami'an DSS sun cafke Mahdi Shehu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na hukumar farin kaya (DSS) sun yi caraf da ɗan gwagwarmayar nan wato Mahdi Shehu.
Jami'an na DSS sun cafke Mahdi Shehu ne asibiti, yayin da iyalansa suka yi ƙorafin cewa ba su sake jin ɗuriyarsa ba bayan hakan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng