'Yan Sanda Sun Samu Nasara, Sun Kawo Cikas ga Ayyukan 'Yan Boko Haram da 'Yan Bindiga

'Yan Sanda Sun Samu Nasara, Sun Kawo Cikas ga Ayyukan 'Yan Boko Haram da 'Yan Bindiga

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta samu nasarar cafke masu samar da babura ga ƴan ta'addan Boko Haram da ƴan bindiga
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar cafke waɗanda ake zargin ne a ƙaramar hukumar Suleja ta jihar Neja
  • Mataimakin sufeto janar na ƴan sanda ya bayyana cewa waɗanda ake zargin suna samar da baburan ne ga ƴan ta'addan a jihohin Kaduna da Neja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta samu nasarar cafke masu samar da babura ga ƴan ta'addan Boko Haram da ƴan bindiga.

Rundunar ƴan sandan ta cafke gungun masu samar da babura ga ƴan ta’addan Boko Haram da ƴan bindiga a jihohin Neja da Kaduna.

'Yan sanda sun cafke masu laifi a Neja
'Yan sanda sun kama masu samar da babura ga 'yan Boko Haram Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Mataimakin sufeto janar na ƴan sanda mai kula da shiyya ta bakwai, Benneth Igweh, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan sa kai sun yi ta'asa a Neja, 'yan sanda sun yi caraf da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Arewacin Najeriya, ƴan ta’adda galibi suna amfani da babura a matsayin ababen hawa wajen sace mutane da kai hare-hare a garuruwa.

Ƴan sanda sun cafke miyagu

Benneth Igweh ya bayyana cewa jami'an rundunar sun cafke mutanen guda uku ne bayan samun bayanan sirri a ƙaramar hukumar Suleja, ta jihar Neja.

Mataimaki sufeto janar na ƴan sandan ya bayyana sunayen waɗanda aka kama a matsayin Shamsuddeen Yunusa, mai shekara 30, Zaharadeen Saidu, mai shekara 25 da Mustapha Haruna, mai shekara 22.

A cewarsa, an ƙwato jimillar babura guda 22, makullan babura da dama, da kuma wayoyin hannu daga hannun waɗanda ake zargin.

Ya ce waɗanda ake zargin sun ƙware wajen kasuwanci da gyara baburan sata, da ake sayarwa ko ba da haya ga miyagu, ciki har da waɗanda ake zargin ƴan Boko Haram ne da ke aiki a sassan jihohin Neja da Kaduna.

Ya bayyana cewa waɗanda ake zargin suna siyarwa da ba da hayar baburan da aka sace a Suleja, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

Masu ba ƴan Boko Haram babura sun shiga hannu

Waɗanda ake zargin suna ba da waɗannan babura ga miyagun da ake zargin ƴan Boko Haram ne da ke addabar sassan jihar Neja da ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

“Shugabansu, Shamsuddeen, ya bayyana cewa yana siyar da baburan akan farashin N200,000 zuwa N250,000."
"Ya ƙara da cewa kwanan nan ya karɓi N250,000 daga hannun wani Ibrahim Kabiru, mazaunin ƙaramar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna, a matsayin wani ɓangaren kuɗin sayen babur ɗin Bajaj."
“Zaharadeen, a gefe guda, shi ne mai jigilar baburan zuwa ga masu saye. Ya amsa da kansa cewa yana kai baburan da yake karɓowa daga hannun Shamsuddeen zuwa ga wani Mustapha a garin Suleja."
"Mustapha Haruna, shi ne bakaniken da ke gyara baburan. Yana gyara baburan da aka sace kafin a miƙa su ga masu siya."

- Benneth Igweh

Ƴan sanda sun musanta cafke Muhuyi Magaji

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya, ta musanta batun cewa ta cafke shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa ba ta cafke Muhuyi Magaji ba, sai dai ta gayyace shi ne domin amsa wasu tambayoyi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng