Izala Ta Yi Martani kan Zargin Raba Sheikh Bin Usman da masallacinsa a Kano
- Rikici ya kunno kai a kan masallaci a jihar Kano tsakanin Sheikh Muhammad Bin Usman da kungiyar Izala inda malamin ya ce ana yi masa wulakanci
- Wanda ya gina masallacin, Alhaji Ado Yahaya Mai Kifi, ya ce sharrin shaiɗan ne ya jawo rikicin kuma ya yi nasiha ga dukkan bangarorin da suke sabanin
- Sai dai a nata bangaren, kungiyar Izala ta Kano ta musanta zargin zaluncin da Sheikh Bin Usman ya yi zargin ana masa a sabon sasallacin Sahaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Bin Usman, ya yi zargi kan cewa an masa wulakanci a masallacin a sabon Sahaba a jihar Kano.
An bude sabon masallacin wata tara da suka gabata, amma malamin ya ce tun lokacin ake nuna masa wariya da wulakanci a bainar jama’a.
A wani rahoto da Freedom Radio ya wallafa a Facebook, kungiyar Izala ta musanta zargin, inda ta ce ana yi wa kowa adalci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya jawo martani daga bangarori daban-daban, ciki har da wanda ya gina masallacin, Alhaji Ado Yahaya Mai Kifi.
A yanzu haka dai ana jira a ga ko gwamnatin Kano za ta dauki matakin kan rikicin kasancewar ita ce ta bayar da izinin gina masallacin kamar yadda shugaban Izala ya tabbatar.
Zargin Sheikh Bin Usman game da masallaci
Sheikh Bin Usman ya bayyana cewa ya yi gum da bakin sa kan abin da ake masa, amma abin ya kai bango inda ya ga ya dace ya fadawa duniya halin da ake ciki.
A cewar malamin:
"Dalibaina suna ga ni ana mani wulakanci a masallacin Sahaba. Abin ya yi yawa har sai da na fito na yi magana."
Sheikh Bin Usman ya bayyana cewa wadanda suke zaluntarsa suna kafa dalili da cewa su gwamnati ta ba wa masallacin.
Bayan hudubar, mutane a kafafen sada zumunta sun fara mayar da martani kan lamarin, suna tambayar karin bayani da kuma irin matakin da za a dauka domin warware matsalar.
Wanda ya gina masallacin ya magantu
Wanda ya sabunta masallacin Sahaba, Alhaji Ado Yahaya Mai Kifi ya bayyana cewa rikicin da ke faruwa ba komai ba ne face sharrin shaiɗan.
Alhaji Ado Yahaya Mai Kifi ya yi kira ga jama’a da su yi addu’a domin samun zaman lafiya da ganin an shawo kan sabanin da aka samu.
"Muna rokon Allah ka da wannan lamarin ya zama fitina a addini. Dole ne masu kula da masallaci su tuna cewa aikin Allah suke yi,
"Kuma kowa zai amsa tambayoyi a gaban Allah dangane da amfanin da ya yi da amanar da aka ba shi."
- Alhaji Ado Yahaya Mai Kifi
Attajirin ya kuma jaddada cewa ya kamata a samar da maslaha tare da warware duk wani sabani cikin lumana.
Martanin Izala kan masallacin sahaba
Shugaban kungiyar Izala na jihar Kano, Hussaini Yakubu Rano ya musanta duk wani zargi da Sheikh Bin Usman ya yi kan wulakanci ko zalunci a masallacin.
Hussaini Yakubu Rano ya ce ba su da masaniya kan wani abu na zalunci a masallacin, ya ce a bisa abin da suka sani komai na tafiya lafiya.
Dr. Jalo ya yi magana kan Qur'anic Festival
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar malaman kungiyar Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi karin haske ka taron Qur'anic Festival.
Sai dai masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi martani ga malamin suna mai cewa taron bai yi kama da wanda sunnah ta koyar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng