Gwamnatin Tinubu Ta Samu Kudi Sama da Naira Biliyan 2 daga Ɗaura Aure a 2024
- Gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar harkokin cikin gida ta samu kuɗin shiga da suka haura Naira biliyan 2 daga ɗaurin aure a 2024
- Ministan cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da hakan da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Talata, 28 ga watan Janairu, 2024
- Ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ɗauki matakan kara karfafa tsaro a iyakokin ƙasar nan wanda zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin gida
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ce ta samu kuɗin shiga kusan Naira biliyan 2.4 a 2024 daga harkokin ɗaurin aure a Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta tara waɗannan maƙudan kudi ne ta hanyar rajistar aure da ke karkashin ma’aikatar harkokin cikin gida.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin wata ganawa da manema labarai, jaridar Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta samu ƙarin kudin shiga
A cewarsa, ma’aikatar ta kuma samu sama da naira biliyan 3.2 daga aikace-aikacen neman izinin kwangilar ‘yan kasashen waje.
Ministan ya ce idan aka haɗa jimulla, an samu karin kashi 150 cikin 100 na kudaden shiga da aka tattara a shekarar 2024.
Wannan ci gaba, a cewar ministan, ya nuna cewa rajistar aure ta zama babbar hanyar samun kudin shiga ga ma’aikatar, wanda ke kara tabbatar da tasirinta a fannin kudaden shiga na kasa.
Tunji-Ojo ya kara da cewa, a shekarar 2023, ma’aikatar ta zarce hasashen kudaden shiga daga ɗaurin aure, inda ta tara sama da Naira miliyan 892 zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2023.
Ya kara da cewa haka a 2024, ma'aikatar ta nunka kuɗin shigar da ta samu daga ɗaurin aurarraki, wanda ya kai kusa N2.4bn, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Wannan ya nuna ci gaba mai kyau a kokarin da ake yi na kara samun kudaden shiga daga bangaren rajistar aure.
Gwamnatin tarayya za ta tsaurara tsaro
Tunji-Ojo ya ce Gwamnatin Tarayya na shirin kara tsaurara tsaro a kan iyakokin kasar domin dakile shigowar bakin haure ba bisa ka’ida ba.
Ya ce shirin zai taimaka wajen ƙara kargin tsaroa a cikin gida da kuma tabbatar da ana doka da oda a sau da ƙafa a Najeriya.
Ministan ya yi alkawarin ci gaba da daukar matakai domin kara inganta ayyukan ma’aikatar cikin gida musamman ta hanyar kara tsaurara tsaro a kan iyakokin kasa.
Haka zalika ya ce za a ɗauki matakai domin sauƙaƙa tsarin ayyukan ma'aikatar cikin gida da kuma lalubo hanyoyin ƙara samuj kuɗaɗen shiga.
NNPCL ta tarawa gwamnati N10trn
A wani labarin, kun ji cewa kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya tara Naira tiriliyan 10 kuma aka saka a su asusun gwamnatin tarayya a shekarar 2024.
Shugaban NNPCL, Malam Mele Kyari ne ya faɗi hakan a lokacin da ya bayyana gaban Majalisar tarayya domin kare kasafin kudin 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng