Rigima Ta Kunno Kai a Kudu kan Kafa Shari'ar Musulunci, An Gano Inda Matsalar Take
Akwai wani yanayi na rashin kwanciyar hankali a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya kan shirin kafa kotunan shari’ar Musulunci a jihohin yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Al’amarin ya tsananta ne a ranar Laraba da ta gabata lokacin da jihar Ekiti ta karbi bakuncin kwamitin shariar Musulunci na farko, karkashin alkalai uku.

Source: Getty Images
Alkalan sun hada da Imam Abdullahi Abdul-Mutolib, Imam Abdulraheem Junaid-Bamigbola da Dr Ibrahim Aminullahi-Ogunrinde, inji rahoton Daily Trust.
Wasu ‘yan gwagwarmayar kasa da masu rajin kare hakkin al’ummar Yoruba sun yi tir da wannan kotun a Ekiti da sauran jihohin Kudu Maso Yamma, suna cewa ba za su amince da kowacce kotun shari’a ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda kafa kotunan Musulunci ya haifar da rudani
Matsalar da ta shafi kafa shari'ar Musulunci a Kudu Maso Yamma ta fara ne da shawarwarin da hukumar shari’a ta kasa (SCSN) ta bayar a jihar Oyo domin kafa kotun Musulunci a garin domin hukunta al’amuran Musulmai.
Duk da cewa SCSN ta ce shari'ar Musulunci ce, yunkurin ya haifar da sabani wanda ya janyo fargaba a cikin jihar yayin da ake zargin akwai wata makarkashiya a kafa kotunan.
Rahotanni sun nuna cewa shawarar kafa kotunan shari’ar Musulunci ta samu nakasu daga rashin fahimta da zuzutawar kafafen sada zumunta.
Mutane suna daukarsa a matsayin wani mataki na kara tsananta shari’a, wanda zai shafi aiwatar da dokokin addinin Musulunci a cikin shari’ar laifuffuka na Kundin Dokar Kuduncin Najeriya.
Duk da haka, bincike ya nuna cewa kotunan shari’ar Musulunci sun dade suna aiki a jihohin Kudu Maso Yamma amma ba su fito fili kamar yadda ake yi a Arewa ba.
Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na Legas, Lawal Pedro, kwanan nan ya bayyana cewa jihar tana da dokar da ta samar da kotun Musulunci.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kan “Wasiyya da Gado”, yana cewa:
“Ba wani sabon abu ne gare mu ba. Muna da doka kuma muna aiwatar da ita. Abin da kawai muke yi shi ne inganta abubuwan da muka riga muka yi.”
A halin yanzu, kotunan shari’ar suna aiki a wurare da dama a Kudu Maso Yamma ciki har da Legas, Ogun, da Oyo, inda suke hukunci kan al’amuran aure, saki da batun raba gado tsakanin Musulmai.
Masu adawa da shari'a sun matsa lamba
Duk da haka, sabon kokarin kafa shari'ar Musulunci a jihar Oyo wanda aka dakatar da shi yanzu ya haifar da tashin hankali a jihar ta Kudu Maso Yamma.
A cewar masu goyon bayan wannan tsari, kafa shari'ar Musulunci zai shafi Musulmai kawai da nufin kare bukatunsu na yau da kullum.
Dukkan al’amuran Musulmai da suka shafi aure, saki, da gado, za a warware su bisa dokokin Al-Qur’ani da Sunnah (tafarkin Annabi) a cikin kotunan Musuluncin.
Duk da haka, adawa da wannan yana ta’azzara daga cikin wadanda ke ganin cewa aiwatar da shari'ar Musulunci jihar zai yi dai dai da yadda ake yi a wasu jihohin Arewa.
Suna zargin cewa shari'ar Musulunci za ta rika yanke hukuncin datse hannu ga barayi da jefe mazinata da yin bulala, wanda suke kallo a matsayin wasu tsauraran dokoki.
Masu adawar sun ikirarin cewa jihohin Kudu Maso Yamma wadanda ke da Kirista, Musulmai da masu bin al’adun gargajiya ba za su iya yar da kafa kotunan shari'a ba.
Matsalar da ta taso daga Oyo zuwa Ekiti
Duk da cewa an dakatar da kafa shari'ar a Oyo, an kafa kotun a Ekiti tare da alkalai uku wadanda suka gudanar da zaman farko a babban Masallacin Ado Ekiti a makon da ya gabata.
Zaman farko da kotun ta yi ya jawo sabani ya tashi lokacin da Ewi na Ado Ekiti, Oba Rufus Adeyemo Adejugbe, a ranar Asabar ya umarci a rushe kwamitin shari'ar.
Ya kuma gayyaci Sheikh Jamiu Kewulere, kuma shugaban kungiyar Imamai da Alfa a Kudu Maso Yamma, Edo da jihar Delta zuwa fadarsa.
Yayin da Sheikh Kewulere ya bayyana cewa an kafa kwamitin domin warware rikice-rikicen al’amuran Musulmai cikin gida, Sarki Rufus ya ce yanayin kasar bai ba da damar yin hakan ba.
"Na fada musu cewa ba sai an kafa kwamitin ba, na ba su umarnin su rushe kwamitin shari'ar daga yanzu.
"Mun rusa kwamitin shari'ar. Idan muka bari irin wadannan kwamitocin suka ci gaba, Kiristoci ma za su so kafa kwamitoci a coci-cocinsu, masu bin al’adun gargajiya ma, wanda zai kai ga rikici."-
- Oba Rufus Adeyemo Adejugbe
Musulmai sun yi adawa da rushe kwamitin kotun
Duk da haka, kungiyoyin Musulmai sun yi tir da rushe kotun da sarkin ya yi, suna cewa rushewar ya take hakkinsu na addini kamar yadda kundin tsarin mulki ya tabbatar.
Kungiyoyin da suka yi adawa da umarnin rushewar sun hada da MURIC; Hukumar Shari’a ta Kasa, majalisar shar'a da MSSN na jihar Ekiti.
Kungiyoyin sun bayyana cewa an kafa kwamitin domin tafiyar da harkokin shari'ar Musulunci da nufin warware al’amuran da suka shafi Musulmi.
MURIC ta bayyana umarnin Sarki Adejugbe a matsayin take hakkokin Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya.
A ranar Lahadi, Farfesa Ishaq Akintola, Daraktan MURIC, a cikin sanarwa ya ce umarnin Oba Adejugbe umarni ne na zalunci.
“MURIC na takaici sosai kan wannan mataki. Umarnin Ewi ya keta doka ta 38(i)&(ii) da ke a Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya wanda ke tabbatar da ‘yancin addini.”
- Farfesa Ishaq.
Hukumar shari’a ta kasa ta bayyana cewa ba kotun shari'ar aka kafa ba, an dai kafa kwamitin sulhu ne don yin sasanci ga Musulmai da suke son warware matsalolinsu a jihar Ekiti, suna cewa gwamnati kawai ke da ikon kafa kotunan shari’ar.
Hukumar, a cikin wata sanarwa daga shugabanta, Alhaji Hammed Afolabi Bakare da Mai, ta ki amincewa da "rushewar" kwamitin, inda ta kara da cewa, “za mu ci gaba da gudanar da addininmu cikin dokokin kasa."
A nata bangaren, kungiyar dalibai Musulmi (MSSN) ta bayyana cewa rushe kwamitin alama ce ta son zuciya da ake nunawa Musulmai a jihar Ekiti.
Injiniya Jimoh Owonifari Kareem, Amir din MSSN a jihar Ekiti, ya jaddada cewa an kafa kwamitin shari'ar ne domin warware rigingimu tsakanin Musulmai bisa ka’idojin addinin Islama.
Duk wani ikirari cewa wannan kwamitin zai kawo illa ga jihar, a ra’ayinmu, yana nuna jin kishin addini ga Islama da Musulmai," inji Injiniya Jimoh.
A lokacin da manema labarai suka tuntube shi, mai magana da yawun kungiyar Musulman Najeriya ta NIMEGG a Kudu Maso Yamma, Mallam Abu Abdullah, ya bayyana cewa ana kafa kwamitocin shari’a domin Musulmai ne kawai.
Ya ce adawar da shari’a tana nuna matakin kiyayya ga Musulmai a cikin kasar Yarbawa, yana cewa:
“A gare mu, ba mu ga wani kungiyar da ke wakiltar Yarbawa ba sai kungiyoyin da aka kafa na musamman daga wadanda ba Musulmai ba domin adawa da Musulunci da Musulmai."
Farfesa Badmus Lanre Yusuf, farfesan ilimin shari’a, ya roki wadanda ke adawa da shari’a a Kudu Maso Yamma da su bar Musulmai su gudanar da addininsu ba tare da matsala ba.
“Idan Musulmai na son shirya bikin aure, to bikin Musulmai ne kawai. Ba a tilasta wa wadanda ba Musulmai su yi bikin aure ko na suna ko na jana’iza bisa shari’a ba.”
- Farfesa Badmus.
"Dalilin da ya sa muke adawa" – Yarbawa
Masu fafutukar ƙasar Yarbawa da suka yi adawa da kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma sun ce ba za shari'a ba za ta iya gyara matsalolin tattalin arziki, siyasa, zamantakewa da al'adu a ƙasar Yarbawa ba.
Sun kuma yi ikirarin cewa jihohin da ke aiki da shari'ar Musulunci a halin yanzu sun zama tamkar "filin yaƙi, rikici, kisan gilla da garkuwa da mutane.
Kungiyar Yarbawan sun kara yin ikirarin cewa kafa shari'ar Musulunci ce ta haddasa wadannan matsalolin, yayin da jihohin su ke da mafi girman matsalolin rashin zaman lafiya a Najeriya.s

Kara karanta wannan
Tinubu: Yadda Gwamnatina ta daure mutane sama da 100 masu daukar nauyin ta'addanci
Gwamna ya magantu kan kafa kotun shari'a
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya ce zai tabbatar ya kare kundin tsarin mulki a rigimar kafa kotunan Musulunci da ta taso a jihar.
"Game da kafa kotun Shari'a a Oyo, idan shirin yana cikin doka, babu matsala, amma idan ba haka ba, zan dauki mataki."
- inji Gwamna Seyi Makinde.
Gwamnan na Oyo ya rantse da Ubangiji cewa zai tsaya tsayin daka wajen kare doka da kundin tsarin mulkin Najeriya yadda ya kamata a wannan magana.
Asali: Legit.ng





