Najeriya na Fuskantar Barazanar Trump, Amurka Ta Toshe Tallafin Lafiya

Najeriya na Fuskantar Barazanar Trump, Amurka Ta Toshe Tallafin Lafiya

  • Gwamnatin Amurka ta dakatar da tallafin PEPFAR na maganin cutar HIV a Najeriya da wasu kasashe masu tasowa
  • Dakatarwar ta biyo bayan umarnin da shugaban Amurka, Donald Trump ya bayar yayin da ya kafa wasu dokoki a lokacin karbar mulki
  • Matakin shugaba Donald Trump zai iya kawo tsaiko ga yaki da cutar HIV a Najeriya, inda miliyoyin mutane ke fama da cutar
  • Legit ta tattauna da wata ma'akaciyar lafiya, Amina Muhammad domin irin tasirin da lamarin zai iya yi ga mutane a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya dakatar da tallafin maganin cutar HIV ta hanyar shirin PEPFAR da ake bayarwa ga Najeriya da sauran kasashe masu tasowa.

Wannan dakatarwa ta shafi kudin da ake amfani da su domin yaki da cutar HIV, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen ceto rayuka da rage yaduwar cutar musamman a kasashen Afirka.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Trump
Dokar Trump za ta shafi harkar lafiya a Najeriya. Hoto: Donal J. Trump
Asali: UGC

Premium Times ta wallafa cewa umarnin dakatar da tallafin ya fito ne daga wata dokar da Trump ya sanyawa hannu a ranar farko da ya kama aiki a matsayin shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dokar ta bukaci dakatar da dukkan kudin tallafin kasashen waje har sai an sake duba tsare-tsaren amfani da su.

Trump ya dakatar da tallafi ga Najeriya

Biyo bayan wannan matakin da Trump ya dauka, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta dakatar da duk wani tallafin kudi da ake bayarwa ta karkashin PEPFAR na tsawon akalla kwanaki 90.

Wannan ya shafi duk wani tallafin kiwon lafiya da ake bai wa kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya.

Rahoton the Guardian ya nuna cewa idan ba a samu wata sassauci ba, PEPFAR na iya dakatar da ayyukansa gaba daya a cikin wata uku masu zuwa.

Tasirin tallafin lafiyan Amurka a duniya

Shirin tallafin na da kasafin kudi na kusan Dala biliyan 6.5 duk shekara, yana bayar da magani ga sama da mutane miliyan 20 da ke fama da cutar HIV/AIDS.

Kara karanta wannan

Trump ya fara farautar baki, za a koro 'yan Najeriya mutane 5,144 gida

Tun lokacin da aka fara shirin, ya ceto rayukan kimanin mutane miliyan 26, in ji rahoton da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar.

Sai dai, a cewar shugaba Trump, ba za su ci gaba da ba da tallafi kai tsaye ba tare da ganin wata moriya ga mutanen Amurka ba.

Matsayarsa ta jawo damuwa daga masana kiwon lafiya da suke tsoron cewa sabon salon mulkin Trump na iya kawo karshen shirin gaba daya.

Tasirin dokar Trump ga Najeriya

Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka fi fama da cutar HIV a duniya, inda kusan mutane miliyan biyu ke dauke da cutar.

Shirin PEPFAR ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da magunguna da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a Najeriya.

Tun lokacin da aka fara shirin, PEPFAR ya zuba sama da Dala biliyan 6 domin tallafawa yaki da cutar HIV a Najeriya, hakan ya taimaka wajen ceto rayukan dubban mutane da rage yaduwar HIV..

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Amma dakatar da shirin na PEPFAR zai kawo tsaiko ga wannan yunkuri, wanda hakan na iya shafar kokarin da ake yi na dakile cutar HIV a Najeriya.

Legit ta tattauna da Amina Muhammad

Wata ma'aikaciyar lafiya a jihar Yobe, Amina Muhammad ta bayyanawa Legit cewa dakatar da tallafin zai iya kawo koma baya ga Najeriya.

'A lokacin da ake kokarin samun nasarar rage illar cutar HIV a Najeriya, dakatar da tallafin ba karamar barazana ba ce.
'Ba kowane mai cutar ba ne zai samu damar sayen magani da sauran abubuwa wanda hakan ma barazana ce ga al'umma baki daya.'

- Amina Muhammad

An fara nemawa Trump wa'adi na 3

A wani rahoton, kun ji cewa an yi muharawa mai zafi a majalisar Amurka kan maganar takarar Donald Trump a wa'adi na uku.

Wani dan majalisar Amurka ne ya bukaci a ba shugaban kasar damar mulki karo na uku domin cigaba da ayyukan alheri a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel