Rigima Ta Barke a Bikin Nadin Sarauta, ana Fargabar An Sumar da Jami'ar NSCDC

Rigima Ta Barke a Bikin Nadin Sarauta, ana Fargabar An Sumar da Jami'ar NSCDC

  • Wasu 'yan daba sun lakada wa wata jami’ar NSCDC duka har ta fadi sumammiya a wani taron nadin sarauta da aka gudanar a Ilorin na jihar Kwara
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami’ar mai ɗa namiji guda tana kokarin hana su karbar kudi daga tsohon dan majalisar wakilai lokacin da lamarin ya faru
  • Sai dai mai magana da yawun hukumar NSCDC ya bayyana cewa abin ya faru ne sakamakon hatsari yayin da aka ce ta fadi daga mota a wurin taron
  • Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da faruwar lamarin wanda ya sha ban-bam da rahoton da hukumar NSCDC ta fada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ilorin, Kwara - Rahotannin sun tabbatar da cewa wasu 'yan daba sun lakada wa wata jami'ar Hukumar Tsaro ta NSCDC duka har ta fadi sumammiya a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Yan sanda a Kano sun sake matsaya kan zargin ta'addanci, sun gano wani shiri a Maulidi

Lamarin ya faru ne a karshen mako yayin bikin nadin sarauta a birnin Ilorin yayin da jami'ar ta so hana matasan karbar kudi daga dan siyasa da ya halarci bikin.

Yadda matasa suka sumar da jami'ar NSCDCa Kwara
Wasu matasa sun yi wa jami'ar hukumar NSCDC dukan kawo wuka yayin nadin sarauta a Kwara. Hoto: @official_NSCDC.
Asali: Twitter

Jami'ar NSCDC ta gamu da tsautsayi a Kwara

Daily Trust ta ce 'yan daban sun yi wa jami’ar mai ɗa namiji guda duka, suna zargin ta hana su karbar kudi daga tsohon dan majalisar wakilai daga Ilorin Gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da lamarin yayin da mai magana da yawun hukumar NSCDC ya fadi sabanin haka.

“Sun lakada mata duka har ta fadi sumammiya, ta samu kumburin fuska da hannuwa, an kai ta asibiti, inda ta farfado daga baya."

- Cewar shaidun gani da ido

Wani mazaunin Ilorin ya bayyana cewa wani abokin aikin jami’ar ya so ya harba bindiga, amma wani ya hana shi saboda yanayin da ake ciki a fadar sarki.

Abin da Hukumar NSCDC ta fada kan lamarin

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun jefa mazauna Benuwai a tashin hankali, sun kashe mutane da dama

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun hukumar NSCDC, Ayoola Michael, ya ce abin ya faru ne sakamakon hatsari a wurin taron.

“Abin da aka fada mani shi ne, hatsari ne dan karami da ya faru yayin da jami'ar ta fado daga motar da take ciki ke tafiya a wurin taron yayin da matasan ke kokarin karbar kudi daga tsohon dan Majalisar.”

Sai dai, Ayoola ya kara da cewa:

“Ba a kama kowa ba tukuna.”

Lamarin ya sanya tsoro a zukatan wadanda suka halarci bikin yayin da aka tsaurara tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da gudun tashin hankali.

Hukumar NSCDC ta tura jami'ar 1,850 Kogi

Kun ji cewa Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta tura jami’ai 1,850 don tabbatar da tsaro a jihar Kogi yayin bukukuwan karshen shekara da aka gudanar.

Kwamandan NSCDC, ta gargadi matasa da su guji aikata laifuffukan da za su iya jawo masu fushin doka yayin bukukuwan saboda zaman lafiyansu.

Kara karanta wannan

Mahdi Shehu ya shiga matsala a hannun DSS, an maka shi a kotu kan zargin ta'addanci

Esther Akinlade, ta kuma nemi al'ummar Kogi da su taimakawa jami'an tsaro da bayanai domin tabbatar da tsaro a fadin jihar baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel