Muhuyi Magaji Ya Yi Magana kan Kamun da 'Yan Sanda Suka Yi Masa, Ya Yi Zargi
- Shugaban hukumar PCACC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Kano, Muhuyi Magaji Rimingado ya yi magana kan kamun da aka yi masa
- Muhuyi Magaji ya bayyana cewa kamun da ƴan sanda suka yi masa na da alaƙa da binciken wani mai laifi da hukumar take yi
- Shugaban na hukumar PCACC ya bayyana cewa ana yi masa cinne na hukumomin tsaro saboda binciken da yake jagoranta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Shugaban hukumar kula da ƙorafe-korafen jama'a da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado, ya yi magana kan kamun da ƴan sanda suka yi masa.
Muhuyi Magaji ya yi zargin cewa ɗaya daga cikin mutanen da hukumarsa ke bincika, ya yi amfani da ƴan sanda don a kama shi.

Source: Facebook
Muhuyi ya yi magana kan cafke shi
Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Morning Brief' a ranar Litinin.
Shugaban na hukumar PCACC ya bayyana cewa kamun da aka yi masa a makon da ya gabata ya shafi aikinsa a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin da bai ba shi mamaki ba, saboda masu cin hanci da rashawa ba za su taɓa bari a zauna lafiya ba.
Muhuyi Magaji Rimingado ya ce akwai hukumomin tarayya daban-daban guda uku da aka cinno masa.
Wane zargi shugaban PCACC ya yi?
Da yake bayanin dalilin kamunsa a makon da ya gabata, shugaban hukumar yaƙi da cin hanci na Kano ya ce lamarin ya shafi zargin wata badaƙala da ta shafi tsohon manajan daraktan kamfanin KASCO.
"Mun gudanar da bincike, kuma mun gano cewa kimanin N4bn na kuɗaɗen gwamnatin jihar Kano sun ɓace ta hannun wani jami’in gwamnati."
“Mun binciki wannan jami’in gwamnati kuma mun ƙwace kadarorin bisa bin ƙa’idojin doka."
"Sashe na 40 na dokar hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar Kano ya ba mu damar yin hakan, kuma mun kai lamarin gaban kotu."

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
“Bayan an gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu kuma aka tsare shi, sai ya fara yin dabaru don karɓe shaidar da ke nuna ya aikata laifin, kuma bai da izinin yin hakan a doka."
"Saboda haka, muka ɗauki matakin canja wurin kadarorin daga inda suke zuwa wani wuri mai aminci don ka da a yi musu katsalandan har sai kotu ta yanke hukunci. Na yi imanin hakan ne ya tayar musu da hankali.”
"Da suka ga ba za su iya jiran hukuncin kotu ba, kuma sun san ba za su yi nasara a shari’ar ba, sai suka shigo da ƴan sanda don su kama ni."
- Muhuyi Magaji Rimingado
Ya ce ƴan sandan da suka je don kama shi sun zarge shi da yin amfani da ƙarfi da shiga wajen da ba shi da hurumi.
Sai dai ya ce ya ƙalubalanci waɗannan zarge-zargen, yana mai cewa doka ta ba hukumar PCACC izinin gurfanar da waɗanda ake zargi da cin hanci a gaban kotu.
Hukumar PCACC ta bankaɗo badaƙala a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar kula da ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado, ya bankaɗo wata badaƙalar satar kuɗaɗe a Kano.
Muhuyi Magaji Rimingado ya ce wasu ƴan siyasa suna yin amfani da ma'aikatun gwamnatin jihar suna yin sama da faɗi da kuɗaɗen jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

