'Yan Bindiga 30 Sun Shiga har cikin Daki Sun Sace Mata da Miji a Abuja

'Yan Bindiga 30 Sun Shiga har cikin Daki Sun Sace Mata da Miji a Abuja

  • 'Yan bindiga sun farmaki unguwar Chikakore da ke Kubwa, sun sace mutum huɗu a cikin gidansu da wani mutum a wata gonar kaji
  • Wata mata ta ji munanan raunuka a kai a sanadiyyar harin, yayin da 'yan sanda suka isa wurin bayan awa guda da faruwar lamarin
  • An ruwaito cewa al’ummar Chikakore sun koka kan rashin caji ofis din 'yan sanda a yankin, suna kira da a samar ofishin jami'an tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun farmaki unguwar Chikakore da ke yankin Kubwa, a karamar hukumar Bwari ta Birnin Tarayya Abuja.

An ruwaito cewa miyagun sun sace wani mutum, matarsa, ɗansu, da wasu mutum biyu a daren Litinin.

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

Abuja
'Yan bindiga sun kai hari Abuja. Hoto: Legit
Asali: Original

Daily Trust ta wallafa cewa wani mazaunin yankin ya bayyana wa manema labarai cewa kimanin mahara 30 dauke da bindigogi samfurin AK-47 ne suka kai harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ruwaito cewa maharan sun isa wurin da misalin ƙarfe 12:00 na dare, kuma kai tsaye suka nufi zuwa gidan wani mutum mai suna Adefija Micheal Akinropo.

Cikakken bayani kan harin Abuja

Vanguard ta wallafa cewa bayan shiga gidan mutumin, 'yan bindigar sun yi garkuwa da shi tare da matarsa, ɗansu da wani ɗan’uwansa.

Bayan farmakin gidan Micheal, 'yan bindigar sun tafi wata gonar kiwon kaji, inda suka yi garkuwa da wani mutum kuma suka ji wa matarsa rauni mai tsanani a kai.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an garzaya da matar zuwa asibiti saboda yawan jinin da ke zuba a jikinta.

Zuwan 'yan sandan Abuja wajen harin

Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda daga ofishin Byazin sun isa wurin bayan awa guda da kai harin, kuma maharan suka tsere da waɗanda suka sace.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Wani mazaunin yankin ya koka da cewa;

“Mun dade muna neman kawo mana caji ofis din 'yan sanda a wannan unguwa, amma ba a ɗauki mataki ba.
"Muna da filin gini da har ma mun kammala ginin ɗakuna biyar domin bai wa 'yan sanda wurin zama, amma har yanzu ba a turo su ba.”

Tarihin matsalar tsaro a yankin

Harin da aka kai a wannan karon ya ƙara jaddada matsalar tsaro a yankin Chikakore, wanda tuni ya sha fama da irin waɗannan hare-hare.

A watan Janairu, wasu 'yan bindiga da suka tsere daga jihar Katsina sun tayar da abubuwan fashewa kusa da wata makarantar Islamiyya a Kuchibuyi da ke yankin Bwari.

Wani mazaunin yankin ya ce;

“'Yan bindigar sun dawo da hare-harensu a Chikakore, kuma al'amarin yana ƙara dagula mana lissafi. Gaskiya muna buƙatar tsaro a nan.”

Matsayar 'yan sanda kan harin

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun sanar da saukar farashin fetur bayan karyewar abinci

Da aka tuntubi jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar 'yan sanda ta Abuja, Josephine Adeh, ta ce tana kan hanya zuwa ofis, kuma za ta tuntubi manema labarai idan ta isa wurin aikinta.

Sai dai, har zuwa lokacin kammala wannan rahoton ba a samu cikakken bayani daga Josephine Adeh ba.

Masu ruwa da tsaki a yankin sun bayyana damuwa kan jinkirin ɗaukar matakan gaggawa domin tabbatar da tsaro a unguwar Chikakore.

Sun kuma nemi hukumomi da jami'an tsaro su tabbatar da kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

An kashe Boko Haram 70 a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar tsaron Najeriya ta yi bayani kan wani farmaki da ta kai kan 'yan ta'addam Boko Haram a jihar Borno.

Kakakin rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa sun kashe 'yan Boko Haram sama da 70 yayin farmakin da suka kai musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel