Bincike Ya Fallasa Yadda 'Yan Majalisa ke Tilasta wa Jami'o'i Biyan Rashawa

Bincike Ya Fallasa Yadda 'Yan Majalisa ke Tilasta wa Jami'o'i Biyan Rashawa

  • Ana zargin wasu kwamitocin majalisun kasar nan da tilasta wa jami'o'in tarayya biyan wasu miliyoyin Naira a matsayin cin hanci
  • 'Yan majalisa sun kulla wani shiri na karɓar Naira miliyan 8 daga kowanne shugaban jami’a don samun amincewar kasafin kuɗi
  • Bincike ya gano yadda wasu daga cikin 'yan majalisar su ke barzana ga shugabannin jami'o'in da hukumar yaki da rashawa ta ICPC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Ana zargin wasu ‘yan majalisa da samar da wani shirin karɓar rashawa daga jami’o’i da sauran manyan cibiyoyin ilimi a ƙasar nan.

An gano cewa yan majalisar suna amfani da barazana da tsoratarwa wajen tilasta wa shugabannin jami’o’i su biya kudin da aka yanke masu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Senate
Ana zargin yan majalisa da wata gagarumar rashawa Hoto: The Nigerian Senate
Source: Facebook

Binciken Premium Times ya gano yadda ‘yan majalisar a wannan karon su ka umarci wasu daga cikin jami’o’I da su biya N8m kowanne don samun amincewar kasafin kuɗinsu na shekarar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake zargi sun hada da Sanatoci da mambobin majalisar wakilai, inda ake amfani da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Ilimi Mai Zurfi da TETFund, da kuma Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimin Jami’o’i wajen aiwatar da lamarin.

Ana zargin ‘yan majalisa da rashawa

Daily Trust ta ruwaito cewa, tsarin da aka ƙirƙira don wannan gagarumin aikin karbar rahsawa ya shafi jami’o’i 60.

An bukaci kowanne shugaban jami’a ya biya Naira miliyan 8 – Naira miliyan 4 ga kowanne daga kwamitocin Dattawa da na Wakilai.

Ana sa ran 'yan majalisar za su samu jimillar N480m, kuma sun ware wasu shugabannin jami’o’i biyu daga Arewa ta Tsakiya da Arewa ta Yamma don karɓar kuɗin domin gujewa tonan silili

Kara karanta wannan

Zargin neman cin hanci daga jami'o'i: Dan majalisa ya fadi yadda abubuwa suka kaya

Majalisa: Shugabannin jami’o’i sun yi korafi

Wani shugaban jami’a, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron abin da ka je ya zo, ya bayyana cewa yan majalisar sun yi masu barazana da su biya kudin.

Ya ce:

“Sun yi mana barazana da bincike idan ba mu bi umarninsu ba. Sun kuma ce yawancin sauran hukumomi suna haɗa kai ba tare da matsala ba,” in ji wani daga cikin shugabannin jami’o’in.

Ana zargin rashawa ta kutsa ICPC

Daya daga cikin shugabannin jami’o’i ya nuna damuwa kan yiwuwar fuskantar karin bincike daga Hukumar ICPC idan bai biya kudin ba, wanda hakan ya ƙara tsananta damuwar su.

A cewar rahoton, wani ɗan majalisa ya ce:

“Ko ICPC tana gabatar da kasafinta a gabanmu. Haka ma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP).”

Da aka tubtubi Demola Bakare, mai magana da yawun ICPC, ya musanta wannan zargi, yana mai cewa:

“Ku na ganin yadda nake dariya. Wannan shi ne karon farko da na ji wannan zargi. Zan bincika idan mun samu labarin makamancin haka.”

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

IGP ya bayyana a gaban majalisa

A wani labarin, kun ji cewa zaman Majalisar Tarayya ya rikice yayin da Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ke gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 a zamanta na ranar Litinin.

An samu sabani a tsakanin 'ya majalisun, inda daya daga cikinsu, Onyekachi Nwebonyi ya nemi takardun kasafin don tabbatar da bayanan sufeton, amma hakan ya kara jawo hatsaniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng