Sojoji Sun Yi Rashi, an Yi Ta'aziyyar Doki Mai Muƙamin 'Sergeant' a Kaduna, an Yaba Hadimarsa

Sojoji Sun Yi Rashi, an Yi Ta'aziyyar Doki Mai Muƙamin 'Sergeant' a Kaduna, an Yaba Hadimarsa

  • Rundunar Sojin Najeriya ta gudanar da jana'iza ta musamman bayan doki Sgt. Dalet Akawala, wanda ya mutu a ranar 24 ga Janairu, 2025
  • Akawala ya kasance ginshiki na al'adun Runduna ta 1, yana da tarihi mai daraja inda aka gabatar da addu'o'i a Kaduna
  • Akawala, wanda ke da muƙamin 'Sergeant' ya fito daga jajirtattun dawaki na farko, ya kuma kawo alfahari ga rundunar kafin mutuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da wani taron jana'iza a ranar Asabar don girmama dokinta, Sgt. Dalet Akawala da ya mutu a ranar Juma'a.

Dokin wanda ke dauke da dimbin tarihi da samar da alfahari ga rundunar ya mutu a ranar 24 ga Janairun 2025 da muke ciki a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Sojoji sun yi jana'izar marigayin doki da ya mutu a Kaduna
Rundunar sojoji ta yi jimamin mutuwar doki mai muƙamin 'Sergeant' a Kaduna. Hoto: Christopher Nanven, Defence Headquarters Nigeria.
Asali: Facebook

Rundunar sojoji ta yi rashin hazikin doki

Punch ta ce taron ya gudana a Hedikwatar Runduna ta 1 da ke Kaduna, karkashin jagorancin Kwamandan Sashen Gudanarwa, Kanal I.A. Akabike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin sa, Akabike ya bayyana Akawala a matsayin ginshikin al'adun rundunar.

Rundunar sojojin ta gudanar da addu'o'i na musamman, inda aka jaddada jaruntaka da kishin da ya kawo wa rundunar.

Laftanar-kanal Musa Yahaya ya bayyana cewa:

"Rundunar Sojojin Najeriya tana jimamin rashin Sgt. Dalet Danfari Akawala, wanda ya kasance mai aminci kuma mai jajircewa a cikin rundunar.
"Marigayi Sgt. Dalet Danfari Akawala ya yi wa rundunar hidima da aminci da jajircewa, ya nuna jarumtaka da juriya.
"Taron yau wata hanya ce ta nuna masa girmamawar karshe, wanda ya kawo alfahari da martaba ga rundunar."

- I.A. Akabike

Hidimar da marigayin doki ya yi ga sojoji

Akawala ya fito daga tsohon dokin rundunar, Sgt. Farin Doki, wanda ya yi hidima daga 1995 har zuwa rasuwarsa a 2011, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Sojoji sun tsananta farautar Bello Turji, ana son kawo karshensa a kwanan nan

Sgt. Dalet, ɗan Akawala, ya ci gaba da hidimar kasancewa mai hidima ga rundunar rundunar daga 2015 har zuwa mutuwarsa, inda aka karrama shi da cikakkiyar martaba ta soja.

Mista Akabike ya mika ta'aziyyarsa ga dukan iyalan dokin da sojojin Najeriya, yana bayyana bakin cikinsa game da wannan babban rashi da aka yi.

Ya yaba wa manyan baki da masu ta'aziyya da suka halarci taron da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Kawo a jihar Kaduna.

Mista Akakibe ya ce:

"An yi addu’o’in neman wanda zai kasance mai kwazo, kuzari, da sadaukarwa don maye gurbin marigayi Sgt. Akawala.”

An yi ajalin kwamandan sojoji a Borno

Kun ji cewa Kwanaki biyu bayan kashe masu kamun kifi 20 a kauyen Gadan Gari na karamar hukumar Bama a jihar Borno, 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun kashe kwamandan soji.

Yan ta'addan sun hallaka wasu jami'ai biyu, da sauran sojoji a sansanin soji na Malam-Fatori, hedikwatar karamar hukumar Abadam a jihar.

Hakan ya biyo fargabar bacewar wasu jami'ai da yan ta'adda suka kai wa sojoji da 'yan sa-kai hari yayin da suke kwaso gawarwakin manoma 40 da aka kashe a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.