Dokar Ta baci: Gwamnan Zamfara Ya Gwangwaje Dalibai 16 da Rikicin Sudan Ya Shafa

Dokar Ta baci: Gwamnan Zamfara Ya Gwangwaje Dalibai 16 da Rikicin Sudan Ya Shafa

  • Gwamna Dauda Lawal ya bai wa dalibai 16 da suka samu jinkirin gama karatu sakamakon rikicin Sudan aiki a gwamnatin Zamfara
  • Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin farfado da karatu a jihar Zamfara
  • Daliban da suka yi karatun jinyar da aka dauka aikin sun sami takardun shaidar kammala karatu daga Sudan bayan kokarin gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Gwamna Dauda Lawal ya baiwa matasa 16 da suka kammala karatun jinya a jami'ar kasa da kasa ta Sudan aiki a gwamnatin Zamfara.

A ranar Alhamis, Gwamna Dauda ya mika takardun shaidar kammala karatu ga matasan a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

Gwamnan Zamfara ya yi magana da ya dauki matasa 16 aikin gwamnati
Gwamnan Zamfara ya ceto karatun dalibai 16, ya ba su aiki a gwamnatin jihar. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Rahoton Zagazola Makama a shafinsa na X ya bayyana cewa gwamnatin Zamfara ta ceto dalibai 66 daga Sudan a 2023 saboda yakin da ake yi a kasar.

Kara karanta wannan

An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamna ya ceto karatun dalibai 16

Daga cikin daliban da aka ceto, 16 sun kasance daliban da ke karantar aikin asibiti da ba su yi jarabawarsu ta karshe ba kafin rikicin na Sudan ya barke.

A watan Satumbar 2023, Gwamna Dauda Lawal ya dauki wani mataki bayan ya tausayawa daliban da aka dawo da su daga Sudan.

Bisa umarnin gwamnan, kwamishinan ilimi na jihar ya tuntubi jami’ar Sudan don shirya jarabawa ga daliban aikin jinyar 16 a Najeriya.

An ce jami'ar kasa da kasa ta Sudan ta aika takardun shaidar kammala karatu na daliban 16, wanda gwamnan ya mika musu a hukumance.

Gwamnan Zamfara ya ayyana dokar ta baci kan ilimi

Gwamnan ya bukaci matasan da su zama jakadu nagari ga jihar Zamfara kuma su shiga cikin shirin gwamnatin don ceto rayuka a jihar.

Mai girma Dauda Lawal ya ce an ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi, domin magance matsalolin ilimi a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Jigawa: Gwamna zai ciyar da mabukata 189, 000 a Ramadan, an ji kudin da zai kashe

"Muna samun ci gaba sosai kuma za mu ci gaba da zuba jari mai yawa a fannin ilimi don samun al'umma mafi kyau," inji gwamnan.

Gwamna ya ba matasa 16 aiki a gwamnatin Zamfara

Gwamnan ya nuna alfahari da nasarar da daliban suka cimma, yana cewa sun jure wahalhalu masu yawa har zuwa kammala karatunsu.

"Muna gina asibitoci a fadin jihar, amma gine-gine kadai ba su wadatar ba; dole sai da ma’aikatan da suke da kwarewa," inji Dauda Lawal.

Gwamnan ya kara da cewa:

"Fannin jinya yana da matukar amfani, kuma saboda haka, za a ba ku aiki kai tsaye a gwamnatin jihar Zamfara."

Gwamnan na Zamfara ya shugaban ma’aikata zai tabbatar da daukar su a matsayin ma’aikatan gwamnatin jihar yayin da ya kuma taya su murna.

Gwamna Zamfara ya gwangwaje ma'aikatan jihar

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince a biya ma'aikatan jihar albashin watanni 13 a cikin watan Disambar 2024.

An ce Gwamna Dauda ya dauki wannan matakin ne domin faranta ran ma'aikata da kuma nuna godiya ga irin namijin kokarin da suke yi na yiwa al'umma hidima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.