Ma'aikata Sun Cika da Murna, Gwamna Ya Fara Biyan Mafi Karancin Albashin N80,000

Ma'aikata Sun Cika da Murna, Gwamna Ya Fara Biyan Mafi Karancin Albashin N80,000

  • Ma'aikatan jihar Oyo sun cika da murna bayan an fara biyansu sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 a watan Janairun 2025
  • Gwamnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta cika alƙawarin da ta dauƙa na fara biyan ma'aikatan sabon mafi ƙarancin albashin
  • Ƙarin albashin ba zai tsaya a kan ma'aikata kaɗai ba, su ma masu karɓar fansho sun samu ƙari kan abin da ake biyansu duk wata
  • Tun da farko da Gwamna Seyi Makinde ya amince da sabon mafi.ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar a watan Nuwamban 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta cikawa ma'aikata alƙawari kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamnatin Oyo ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000, inda ta raba naira biliyan 12 ga ma’aikatanta don cika alƙawarin da Gwamna Seyi Makinde ya ɗauka.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

Gwamnan Oyo ya biya sabon albashi
Gwamnatin Oyo ta fara biyan sabon albashin N80,000 Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Dotun Oyelade, ya bayyana hakan, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Oyo ya biya albashin N80,000

Dotun Oyelade ya tabbatar da cewa gyaran albashin ya shafi dukkanin matakan ma’aikata, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ma’aikatan da ke matakan albashi na ɗaya zuwa na shida yanzu suna karɓar ƙarin N50,000, yayin da waɗanda ke matakin albashi na 17 suka samu ƙarin sama da N180,000.

Masu karɓar fansho ma sun amfana daga sabon tsarin albashin, inda mafi ƙarancin fansho aka tsayar da shi kan N25,000 tare da yin ƙarin kaso 33% ga ma'aikatan da suka yi ritaya guda 40,000.

Don rage ɗawainiyar kashe kuɗi, gwamnatin ihar ta soke kudin N4,000 na siyan fom ɗin ritaya, wanda ake sa ran ma’aikata 4,500 da ke dab da yin ritaya za su ƙi kashe kusan Naira miliyan 20 wajen siya.

Ma'aikata sun yi murna

Haka kuma, daya daga cikin ma’aikatan jihar Oyo, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa an biya sabon mafi ƙarancin albashin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto zai cikawa ma'aikata alkawari, ya fadi lokacin fara biyan N70,000

"Eh, an biya sabon mafi ƙarancin albashi jiya, kamar yadda gwamna ya yi mana alƙawari. Mun yi mamaki tare da farin ciki a lokaci guda."

- Wata ma'aikaciya

Idan ba a manta ba dai Gwamna Seyi Makinde ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi a watan Nuwamban 2024.

Gwamna Makinde ya naɗa sabon sarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da naɗa sabon Alaafin na Oyo, bayan shekara biyu ana jira.

Gwamna Seyi Makinde ya amince da naɗin Yarima Abimbola Awoadea matsayin sabon wanda zai riƙe sarautar Alaafin na Oyo.

Naɗin Yarima Abimbola Awoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo ya biyo bayan bincike mai zurfi da majalisar masu naɗa sarki ta Oyomesi ta gudanar.

Yarima Abimbola Awoade zai maye.gurbin tsohon Alaafin, Oba Lamidi Adeyemi III, wanda ya rasu a ranar 22 ga Afrilu, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng