'Ka Yi Kokari': Kiristocin Arewa Sun Bukaci Babbar Kujera daga Tinubu, Sun Zargi Take Hakkinsu
- Kungiyar Kiristoci ta Arewa ta yaba da tsarin gwamnatin Bola Tinubu da take tafiya da kowa, amma ta nemi karin wakilcin Kiristoci a manyan mukamai
- Shugaban kungiyar, Rabaran Yakubu Pam ya ce, duk da gwamnatin Musulmi-Musulmi, akwai kyakkyawar dama ga kowa, amma akwai bukatar Kirista a matsayin mataimakin shugaban kasa
- Kungiyar ta bukaci gwamnatin Tarayya da ta kara himma wajen kawo zaman lafiya, yaki da yunwa, da tabbatar da adalci ga dukkannin 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja- Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihohi 19 na Arewa da Abuja ta yaba wa salon mulkin Bola Tinubu.
Kungiyar ta bayyana cewa gwamnatin Musulmi-Musulmi na Bola Ahmed Tinubu ta nuna tsarin tafiyar gwamnati da kowa.

Asali: Facebook
Kiristocin Arewa ta koka da nuna wariya
Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda wasu jihohi a Arewa ke neman take musu hakki musamman ta bangaren gina coci-coci, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban CAN na Arewa, Rabarna Yakubu Pam, ya ce duk da gwamnatin Musulmi da Musulmi ne amma akwai bukatar cusa Kiristoci sosai a ciki.
"Duk da tsarin Musulmi-Musulmi, muna ganin akwai karbuwa ga kowa, amma muna bukatar Kirista a matsayin mataimakin shugaban kasa."
- Yakubu Pam
Kiristoci sun bukaci manyan mukamai daga Tinubu
Pam ya kara da cewa, duk da haka, gwamnatin na da bukatar tabbatar da cewa dukkan bangarorin Najeriya sun samu wakilci domin nuna bambancin addini.
Rabaran Pam ya ce matsalar tsaro da garkuwa da mutane na ci gaba da addabar jama’a, inda ya bukaci gwamnati ta dauki matakan gaggawa don magance matsalolin.
“An shigar kowa a cikin mulki,” duk da kasancewar tsarin shugabancin Musulmi-Musulmi ne.
“A wurina, abu mafi muhimmanci shi ne gwamnati mai daukar kowa da kowa, kuma duk da cewa sun yi tikitin Musulmi-Musulmi, mun ga wani mataki na adalci wajen shigar da kowa.

Kara karanta wannan
"Za mu gyara inda ya kamata": Shettima ya lissafa muhimman ayyukan gwamnatin Tinubu
“Amma a bangarenmu, za mu ce ‘eh, ya dace mu samu Kiristoci a wasu mukamai kamar mataimakin shugaban kasa da sauran wurare domin nuna bambancinmu.
“Mun san burin jama’a shi ne ganin an magance matsalar rashin tsaro domin su sami damar gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum ba tare da tsoro ba.”
- Yakubu Pam
Gwamnatin Tinubu ta sha alwashin kawo sauyi
Shugaban ya kuma koka kan yadda wasu jihohi a Arewa ke hana Kiristocin Arewa damar mallakar filaye don gina coci da kuma rashin wakilci a mukaman gwamnati, Punch ta ruwaito.
Christopher Tarka, wanda ya wakilci Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ya ce Tinubu zai ci gaba da yin aiki don tabbatar da adalci da zaman lafiya a Najeriya.
Kiristocin Arewa sun goyi bayan kudirin haraji
Kun ji cewa Kungiyar Kiristocin Arewa ta yi watsi da zargin cewa kudirin harajin shugaba Bola Tinubu yana adawa da yankin Arewa.
CHAIN ta bayyana haka ne yayin gudanar da wani taron tattaunawa a jihar Kaduna kan batun haraji da tasirinsa ga al’umma.
Shugabannin kungiyar sun yi kira da a rungumi gaskiya tare da bayar da gudunmawa wajen gina kasa mai inganci.
Asali: Legit.ng