Ana Jiran Kashe Bello Turji, Sojoji Sun Sheke Hatsabibin Kwamandan Yan Ta'adda
- Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da dakarun sojojin Najeriya suka samu a makon da ya gabata
- Daraktan yaɗa labarai na DHQ ya bayyana cewa sojojin sun samu nasarar hallaka wani hatsabibin kwamandan ƴan ta'adda mai suna Abu Mosaje
- Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa sojojin sun kashe ƴan ta'adda 96 a faɗin ƙasar nan tare da ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun kashe wani fitaccen kwamandan ƴan ta’adda kuma mai safarar makamai mai suna Abu Mosaje a jihar Plateau.
DHQ ta bayyana cewa dakarun sojojin sun kuma kashe wasu ƴan ta'adda 96 a faɗin ƙasar nan a makon da ya gabata.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar a ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun taso ƴan ta'adda a gaba
Manjo Janar Edward Buba ya ce sojoji sun ƙara ƙaimi a ayyukan yaƙi da ta’addanci a faɗin ƙasar nan, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Ya bayyana cewa a yanzu sojoji sun maida hankali ba kawai kan ƴan ta’addan ba, har ma da masu ba su goyon baya, da masu basu bayanai.
A cewarsa, sojojin sun kashe Abu Mosaje a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau.
Manjo Janar Buba ya kuma bayyana cewa sojojin sun kama wani shahararren mai garkuwa da mutane mai suna Babangida Usman a ƙaramar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.
Daraktan yaɗa labaran na DHQ ya ce Babangida Usman yana cikin jerin sunayen ƴan ta'addan da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo.
Dakarun sojoji sun samu nasara kan miyagu
“Haka kuma, sojoji sun kama wani shahararren mai safarar makamai da ɗansa, masu suna Timothy Yusuf da Timothy Obadiah."
“A yankin Kudu maso Gabas, sojoji sun kama ƴan ta’addan IPOB/ESN guda bakwai, ciki har da wani shahararren mai garkuwa da mutane da mai ba da bayanai, a ƙananan hukumomin Enugu ta Arewa da Ehime Mbano na jihohin Enugu da Imo."
"Haka zalika, a cikin makon da ake bita, sojoji sun kashe ƴan ta’adda 79 tare da suka kama mutane 224."
“Sojoji sun kuma kama mutane 28 masu satar man fetur tare da ceto mutane 67 da aka yi garkuwa da su."
- Manjo Janar Edward Buba
Manjo Janar Edward Buba ya ƙara da cewa sojojin da ke yankin Kudu Maso Kudu sun hana ɓarayin man fetur samun kimanin naira miliyan 747 a cikin makon.
Ya ce sojojin sun gano tare da lalata tukunyar dafa ɗanyen mai guda 215, ramukan ajiye mai guda 26, jiragen ruwa guda 29, tankunan ajiya guda 62, ganguna guda 20, da wuraren tace mai guda 42.
Sojoji sun yi ƙoƙari
Abba Tukur Sale ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da dakarun sojoji suke samu a kan ƴan ta'adda abin a yaba ne.
Ya yaba kan yadda sojoji suke ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen miyagun da ke barazana ga tsaron ƙasar nan.
"Eh gaskiya muna yabawa da irin nasarorin da sojoji suke samu a kan ƴan ta'adda. Suna yin namijin ƙoƙari sosai. Muna fatan Allah ya ci gaba da ba su nasara."
- Abba Tukur Sale
Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga dauƙe da makamai sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kauru da ke jihar Kaduna.
Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba ɗaya da wasu mutane biyar zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng


