Su Waye Ke Daukar Nauyin Ta'addanci? Hafsan tsaro Ya Fayyace Gaskiya kan Lamarin

Su Waye Ke Daukar Nauyin Ta'addanci? Hafsan tsaro Ya Fayyace Gaskiya kan Lamarin

  • Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro, musamman yadda ake samun yan ta’adda da kudaden kasashen ketare
  • Janar Musa ya ce akwai wasu da ke daukar nauyin ta'addanci, ciki har da kudaden da ake samu ta garkuwa, fashi, da haramtattun hanyoyi
  • Hafsan tsaron ya yi kira da a hada kai domin kawo karshen matsalolin tsaro, yana mai jaddada cewa Najeriya ta yi nasara kan ta'addanci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi magana kan tabarbarewar tsaro.

Janar Musa ya tabo maganar daukar nauyin ta'addanci da ya yi kamari musamman a Arewacin Najeriya.

Hafsan tsaro ya fadi yadda yan ta'adda ke samun kudi
Janar Christopher Musa ya koka kan yadda matsalolin tsaro ke kara ƙamari. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Gwamnati ta yi magana kan sulhu

Janar Musa ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a daren jiya Juma'a 24 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta kawo shirin yin sulhu da 'ƴan bindiga domin samun tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Gwamnatin ta buƙaci gwamnatin jihar Katsina da ta goyi sabon shirin wanda zai sanya ƴan bindiga su ajiye makamansu tare da sako mutanen da suka sace.

Sai dai a wani bangaren, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ba zai nemi ƴan bindiga domin su zo a yi sasanci da su ba.

Yadda yan bindiga ke samun kudin shiga

Hafsan tsaron ya koka kan yadda suke samun yan ta'adda da kudaden kasashen ketare wanda ya jefa shakku kan ayyukansu.

Da aka tambayi Janar Christopher Musa kan su waye ke daukar nauyin ta'addanci, shugaban tsaron ya kada baki ya ce:

"Wannan ita ce tambaya mafi tsada, su waye ke daukar nauyinsu, wani lokaci suna samun kuɗi da garkuwa da mutane, fashi da sauran abubuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

"Ba za ka iya fatali da hakan ba, saboda akwai lokacin da muka kama su mun samu kudaden kasashen waje."

- Cewar Kamar Musa

Matsalolin sojoji a yaki da ta'addanci

Hafsan tsaron ya ce akwai wasu da dama a kasashen ketare da ke gaba da Najeriya musamman kan matsalar tsaro.

"Muna fuskantar matsaloli duk lokacin da muka samu labarin nahiyar Bello Turji kafin mu je ya tsere.
"Akwai wadanda ke ba shi bayanai, muna samun labarin a cikin awanni biyu ya samu labarin ya gudu.
"A yanzu haka ya fara neman hanyar da za a bar duka wadannan abubuwa yana son ya ajiye makamansa."

- Janar Christopher Musa

Janar Musa ya bukaci hadin kai domin kawo karshen matsalolin inda ya ce an taba hasashen Najeriya ba za ta wuce 2015 ba.

Ganduje ya ba sojoji shawara kan ta'addanci

Kun ji cewa shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci sojoji su inganta salon aikinsu ta hanyar mamaye dazuzzuka domin kakkabe 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron

Ganduje ya tuna yadda aka fatattaki 'yan bindiga daga dajin Falgore a Kano ta hanyar amfani da dajin a matsayin sansanin soja.

A hannu daya, Gwamna Umar Bago ya fadawa gwamnatin tarayya dabarar kiyaye hadurra da kuma inganta tsaron al'ummar Niger.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel