Wata Sabuwa a Kano, an Kama Shugaban Hukumar PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado

Wata Sabuwa a Kano, an Kama Shugaban Hukumar PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado

  • Ƴan sanda sun yi ram da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado
  • Wata majiya daga hukumar ta tabbatar da kama Rimingado, ta ce ana shirin maida shi babban birnin tarayya Abuja
  • Ana zargin dai kama Muhuyi ba zai rasa nasaba da shari'o'in cin hanci da ya buɗe wa manyan mutane a jihar Kano ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Rahotanni sun nuna cewa an kama shugaban hukumar kula ƙorafe-ƙorafe da yaki da cin hanci ta Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado.

Wani majiya a hukumar ta tabbatar da lamarin da cewa, “Tabbas an kama shi a yau (Jumma’a), kuma ana sa ran za a kai shi Abuja.”

Muhuyi Magaji Rimingado.
Yan sanda sun kama shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji Rimingado Hoto: Muhuyi Magaji
Source: Facebook

Yan sanda sun kama Muhuyi Magaji

Rahotan Daily Trust ya nuna cewa kamen ya biyo bayan zuwan ‘yan sanda karkashin ASP Ahmed Bello, wanda ya nace cewa yana da umarnin tsare Rimingado.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta bayyana cewa da yiwuwar kama Muhuyi Rimingado na da nasaba shari’ar da ake yi kan tsohon Manajan Darakta na kamfanin rarraba kayan noma na Kano (KASCO), Bala Muhammed Inuwa.

Hukumar PCACCC na tuhumar Bala Inuwa da karkatar da kudaden jama’a har naira biliyan hudu (N4bn).

An fara shari’ar ne a watan Nuwamba 2023 a Babbar Kotun Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Hafsat Yahaya.

Dalilin da ya sa aka kama Muhuyi Magaji

Kotun ta ba da umarnin kwace kadarorin da ake zargin suna da nasaba da lamarin, ciki har da kudaden da ke cikin asusun banki gabanin yanke hukunci.

A watan Disamba 2023, Bala Muhammed Inuwa ya shigar da wata kara daban a gaban Mai Shari’a Aisha Ya’u a Babbar Kotun Kano.

Ya nemi a cire ‘yan sandan da ke tsare kamfanin Limestone Processing Links Ltd., inda aka ajiye dukiyoyin da aka kwace. Mai Shari’a Aisha Ya’u ta amince da hakam.

Kara karanta wannan

'Na samu lafiya,' Buhari ya fadi kalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa

Sai dai hukumar PCACC ta nuna rashin jin dadinta cewa ba a sanar da ita ba game da karar ba kuma ba a sa ta a shari'ar ba duk da ita ke da hurumin tsare kadarorin.

Bisa haka, PCACC ta shigar da roko don dakatar da aiwatar da umarnin kotu, tare da neman sanya ta cikin shari’ar, tana mai jaddada cewa aikin ‘yan sandan shi ne kawai su kula da tsaron kayayyakin

Mutanen Kano sun fara magana

Makonni biyu da suka wuce, a taron manema labarai, Rimingado ya bayyana cewa hukumarsa ta dakile yunkurin fitar da dukiyoyin da aka kwace na N2bn.

A halin yanzu dai kama Muhyi Magaji Rimingado ya haifar da ce-ce-ku-ce da tambayoyin da babu amsa kan dalilin daukar wannan mataki.

Wasu Kanawa na ganin kama shi ba zai rasa alaƙa da manyan mutanen da ya taso da zargin cin hanci a jihar Kano ba.

Shugaban PCACC ya matsawa mutanen Ganduje

Kun ji cewa tsohon Manajan Daraktan KASCO, Bala Inuwa ya nuna ɓacin ransa kan matakin hukumar PCACC na ƙin bin umarnin kotu.

Hukumar PCACC ta na zargin Bala Inuwa da mallakar wasu kadarori ta hanyar almundahana da kudin fa ya samu ta haramtacciyar hanya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262