Bello Turji Ya Sake Sauya Mafaka, an Gano Shi da Wasu Rikakkun Yan Ta'adda 2, Ya Nadi Bidiyo

Bello Turji Ya Sake Sauya Mafaka, an Gano Shi da Wasu Rikakkun Yan Ta'adda 2, Ya Nadi Bidiyo

  • Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa an gano rikakken dan ta'adda, Bello Turji a wani yanki a jihar Zamfara
  • An tabbatar da kasancewar Bello Turji, shugaban ‘yan bindiga, a dajin Kalage, yankin Mashema na Kagara ta Gabas, jihar Zamfara
  • Majiyoyi sun nuna cewa Turji yana aiki tare da mukarrabansa biyu, 'Office da Ibrahim Buzu' a wannan yankin
  • Bello Turji da mayakansa suna da sansani mai karfi a cikin dajin, suna tare da dabbobi da aka kwace daga hare-haren da suke kaiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - Majiyoyi masu sahihanci sun tabbatar da kasancewar Bello Turji, shugaban ‘yan bindiga, a dajin Kalage bayan zargin yana wani yanki na daban.

Dajin da ake zargin dan ta'addan ya boye na yankin Mashema ne a Kagara ta Gabas da ke jihar Zamfara a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Majiyoyi sun gano inda Bello Turji ya sake tserewa a Zamfara
Yayin da ake zargin Bello Turji na mahaifar Bello Matawalle, dan ta'addan ya sake mafaka. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

An zargin Turji ya shiru bayan hare-hare

Rahoton Zagazola Makama ya ce an samu bayanai cewa Turji yana aiki tare da mukarrabansa guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da shugaban 'yan bindiga, Bello Turji ya yi shiru kwanan nan, bayan da aka tsananta kai hare-hare kan sansaninsa a yankin Arewa maso Yamma

Turji wanda ya saba amfani da bidiyo wajen nuna karfinsa, bai bayyana a bainar jama’a ba, lamarin da ya sanya tambayoyi a zukatan al'umma

Rahotanni sun ce Turji ya saki wasu mutanen da aka yi garkuwa da su domin rage zafin hare-haren sojoji a yankinsa.

Malami yana kokwanton kisan ɗan Bello Turji

Duk da haka wasu rahotanni na tabbatar da cewa sojoji sun hallaka ɗan Bello Turji a wani da suka kai maboyarsu inda mayakansa da dama suka rasu.

Sai dai wani malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada yana kokwanton kisan inda ya ce bai tsammanin Bello Turji yana da yaro mai shekaru kamar wanda ake yaɗawa.

Kara karanta wannan

Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin

Ana zargin Turji ya sake mafaka a Zamfara

An tabbatar da cewa daga cikin wadanda ake hasashen na kusa da dan ta'addan ne an bayyana sunayensu da Office da Ibrahim Buzu, cewar rahoton Daily Post.

Turji da mukarrabansa sun kafa sansani mai karfi a cikin dajin tare da mayaka dauke da makamai da dabbobi da aka kwace daga hare-haren da suke kaiwa.

A ranar Alhamis 23 ga watan Janairun 2025, Turji ya dauki bidiyo, amma ya ki sakin shi saboda tsoron a gano matsayinsa sannan a kai masa hari daga sama.

Ana zargin Turji ya tsere mahaifar Matawalle

Kun ji cewa ana zargin cewa shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, yana cikin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara yayin da sojoji suka kara matsa masa.

Rahotanni sun ce an ga mabiyan Turji suna hijira a kan babura, dauke da raunana, zuwa wuraren Garsa/Kadanya a ranar 19 da 20 ga watan Janairun 2025

An yi zargin cewa Turji yana boye tare da wasu mabiyansa a Garsa/Kadanya, tare da goyon bayan tsohon abokin gaba, Jummo Smally.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.