"A Bar Mu da Talaucinmu": Shettima Ya Fadi Matsayarsa kan Dogara da Tallafin Turawa

"A Bar Mu da Talaucinmu": Shettima Ya Fadi Matsayarsa kan Dogara da Tallafin Turawa

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa bai yarda da dogaro da tallafin ƙasashen waje ba
  • Sanata Kashim Shettima ya bayyana haka ne a taron tattalin arziki na duniya da ke gudana a Davos-Klosters, Switzerland
  • Ya shawarci kasashen Afrika da su yi kokari wajen cin moriyar dimbin albarkatun da su ke da su su, tare da neman masu zuba jari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa bai yarda cewa tallafin ƙasashen waje shi ne mafita ga matsalolin tattalin arziki na ƙasashe masu tasowa ba.

Shettima ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis 23 ga watan Janairun 2025 yayin taron tattalin arziki na duniya (WEF) 2025 da ake gudanarwa a birnin Davos-Klosters, Switzerland.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Kashim
Kashim Shettima ya wakilci Najeriya a taron tattalin arziki na duniya Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

Jaridar The Cable, ta ruwaito cewa taron WEF dandali ne da ke haɗa shugabannin gwamnati, masana’antu, jami’o’i, da kungiyoyin farar hula don tattauna manyan matsalolin duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin tattaunawa a wani zaure, Shettima ya yi tsokaci kan bukatar zuba jari a ilimi, tallafawa mata, da kuma zuba jari a fannin kirkire-kirkire domin sake fasalin al’ummomin Afrika.

Najeriya ta ce akwai albarkatu a Afrika

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa, Kashim Shettima ya bayyana muhimmancin ƙasashen Afrika su yi amfani da albarkatunsu wajen jagorantar ci gaban duniya.

Ya ce duk da akwai kalubale a Najeriya, amma ce matsalolin tattalin arzikin suna samar da wata dama ta musamman don kafa tubali mai ƙarfi na ci gaba.

Shettima ya ce:

“Tabbas, muna da matsaloli, amma sun zo da damarmaki da za su taimaka wajen sake gina al'umma."
“Wannan ya ba mu wata dama ta musamman, wata kofa don zuba jari wajen bunkasa mutane, musamman kan ilimi, tallafawa mata, aikin gona da fasaha, da haɓaka tattalin arziƙinmu zuwa zamani."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Matsayin Shettima a kan tallafin ketare

Mataimakin shugaban ƙasa ya bayyana matsayinsa na kin amincewa da dogaro da tallafi daga ƙasashen waje zuwa Najeriya.

Ya ce:

“Ba na yarda da tallafi, ina yarda da haɗin kai. Zan fi son ɗaukar talaucina da mutunci kuma in yi hulɗa da mutane, ƙasashe, da kamfanoni a matsayin masu daidaito, ba a matsayin bawa da shugaba ba."
“Nahiyar Afirka ita ce mafi arziki a duniya, kuma tafarkin ci gaban duniya yana fuskantar Afrika, Najeriya za ta taka rawar gani ko ta gaza a wannan tafiya."
“Saboda haka, na shigo da kwarin gwiwa, da kyakkyawar fata don gobe mai kyau, amma mafi mahimmanci, na yarda cewa matasan Afrika su ne ginshikin canjin Nahiyar.”

Shettima ya shilla kasar waje

A baya, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya shilla ƙasar Switzerland don wakiltar Najeriya a taron shekara-shekara na Majalisar Tattalin Arzikin Duniya (WEF) na 2025.

Taron ya gudana ne a Davos-Klosters, inda shugabanni daga fannoni daban-daban suka hallara don tattauna manyan matsalolin duniya, wanda ya jawo hankalin shugabannin duniya daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.