"Na Yi Rashin Babban Amini," Buhari Ya Yi Ta'aziyyar Mutuwar Abokinsa na Kud da Kud
- Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna jimami bisa rasuwar Da Yohanna Dalyop, yana mai cewa ya rasa wani amininsa na kud da kud
- Buhari ya bayyana marigayi Dalyop a matsayin injiniya da ya ƙware, fasto mai aminci wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bincike da ƙirƙire
- Tsohon shugaban ya yaba wa gudunmawar marigayin wajen warware matsalolin makamashi a Najeriya, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai da abolkansa
- Muhammadu Buhari ya kara ce ba za a iya mantawa da gudunmawar da Dalyop ya bayar, musamman a fannin makamashi da inganta rayuwar jama'a
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina - Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya nuna jimami bisa rasuwar Da Yohanna Dalyop, yana mai cewa ya rasa wani amininsa na kud da kud.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2
Tsohon Shugaban ya bayyana marigayi Da Yohanna Dalyop a matsayin amini mai aminci da kuma ƙwaƙwalwa mai kaifin basira, wanda ya ba da gudunmawa.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Mallam Garba Shehu, ya fitar a ranar Juma’a kuma aka wallafa a shafinsa na X, tsohon Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamacin.
Buhari ya yi ta’aziyya kan rasuwar Dalyop
Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Dalyop da dan kasa na gari da ya sadaukar da rayuwarsa wajen binciken don ci gaban al'umma.
Ya kara da bayyana shi da matsayin fasto kuma injiniya da ya ƙware, wanda ya sadaukar da mafi yawan aikinsa wajen bincike da ƙirƙiro hanyoyin samar da makamashi.
Babban rashi da Buhari ya yi a Plateau
Muhammadu Buhari ya ce:
“Da rasuwar Yohanna Dalyop, na rasa wani amini, wanda na samu damar saninsa tsawon shekaru da dama."
Fahimtarsa kan al’amura da ƙwarewarsa musamman a bangaren makamashi ba su da na biyu."
Buhari ya yi jinjina ga gudunmawar Dalyop
Tsohon shugaba Muhammadu ya taya iyalan marigayin, abokan arziki, abokan sana’a, da kuma gwamnati da al’ummar Jihar Filato jimamin babban fasto kuma injiniya.
Tsohon shugaban ya tuna yadda Dalyop ya samu nasarar warware kalubale masu yawa da suka shafi makamashi a ƙasar.
“Mutum ne mai hangen nesa da ƙwaƙwalwa ta musamman, rashinsa abin bakin ciki ne matuƙa."
Buhari ya yi jimamin fashewar tanka
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi taka-tsan-tsan kan masifun da ke afkuwa bayan faduwar tankar fetur.
Tsohon shugaban ya bayyana damuwarsa inda ya gargadi jama'a da su rika daukar matakan kare rayukansu daga irin wadannan bala'o'in da ke afkuwa a titunan kasar nan.
Buhari ya yi kira ga mahukunta a Najeriya su kara himma wajen wayar da kan jama’a game da mahimmancin bin umarnin, musamman kan haɗarin da ambaliyar ruwa da sauran iftila’i za su iya haifarwa.
Asali: Legit.ng
