An Kama Matar Aure Tana Lalata da Saurayi a Abuja, Kotu Ta Yanke Masu Hukunci

An Kama Matar Aure Tana Lalata da Saurayi a Abuja, Kotu Ta Yanke Masu Hukunci

  • Wata kotun Gwagwalada ta tsare Mohammed Nazifi da Bilkisu Ibrahim a gidan gyaran hali na Suleja har zuwa ranar 29 ga Janairu
  • Bilkisu Ibrahim ta shaidawa kotun cewa ta yi zina da Nazifi duk da kasancewarta matar aure amma shi bai san hakan ba
  • Mai shigar da kara ya ce laifin su ya saba da kundin laifuffuka sashe na 387 da 388, wanda ya haramta aikata zina da laifuffukan iyali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata kotun majistare a Gwagwalada da ke Abuja, ta yanke hukunci kan wasu masoya biyu, Mohammed Nazifi da Bilkisu Ibrahim.

Kotun karkashin jagorancin majistare Olatunji Oladunmoye ya ba da umarnin tsare masoya biyu a gidan gyaran hali na Suleja.

Kotu ta hukunta matar aure da saurayinta da aka kama suna lalata a Abuja
Abuja - Wata matar aure da saurayinta sun amsa laifin sun yi zina amma suna neman kotu ta yi sassauci. Hoto: High Court
Asali: UGC

An gurfanar da matar aure da saurayi a kotu

Alkali Olatunji Oladunmoye ta ce a tsare Mohammed da Bilkisu har zuwa ranar 29 ga Janairu, lokacin da za a yanke hukunci, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masoyan, Nazifi mai shekaru 30 da Bilkisu mai shekaru 25, mazauna kauyen Gui a titin filin jirgin sama na Abuja, sun amsa laifin aikata zina da aka tuhume su da shi.

Nazifi ya roki kotu da ta yi masa sassauci, yana mai cewa bai san cewa Bilkisu matar aure ce ba a lokacin da suka aikata laifin.

Matar aure ta amsa laifin yin zina da saurayinta

Bilkisu ta tabbatar da maganar Nazifi, inda ta ce ta yi zina da shi ba tare da bayyana masa cewa ita matar aure ba ce ba.

Bilkisu ta ce:

“Na san cewa a al’ada ta, laifi ne ka yi lalata da duk namijin da ba mijinki ba. Ni Musulma ce, na san cewa laifi ne yin zina alhalin ina da aure.
"Har yanzu dai ni matar wanda ya shigar da karar ce, kuma muna da ƙaramin yaro mai shekara uku tare."

Kara karanta wannan

'Rayuwar IBB': Tsohon shugaban Najeriya zai fitar da littafin da aka dade ana jira

Matar ta ce ta roki mijinta, Dayabe Abdullahi da ya yafe mata cin amarsa da ta yi, sannan ta roki kotu ta yi mata sassauci kan wannan laifi.

Mai shigar da kara ya fadi laifin masoyan

Tun da fari, mai gabatar da kara, Dabo Yakubu, ya bayyana cewa mijin Bilki ya kai karar ne a ofishin ‘yan sanda na Gwagwalada.

Yakubu ya ce wadanda aka kama sun amsa laifinsu a cikin bayanansu ga ‘yan sanda, inda suka tabbatar da aikata zinar da ake tuhumarsu da ita.

Ya bayyana cewa laifin ya saba da sashe na 387 da 388 na Kundin Laifuffuka, wanda ke haramta zina da laifukan da suka shafi iyali.

"Na kama mijina yana lalata da matar aure"

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata mata, Rebecca Adeniyi ta shaida wa kotun gargajiya da ke Igando, Legas, cewa ta kama mijinta, Yusuf, yana aikata zina da matar aure.

Rebecca ta ce mijinta ya gina wani Masallaci amma ya mayar da shi wurin aikata mummunar lalata da matan aure da ma marasa aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.