Zina da Matar Aure ba laifi ba ne - Wata Babbar Kotun Kasar Indiya ta zartar da Hukunci
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, a ranar yau ta Alhamis wata babbar kotun kasar India ta zartar da sabon hukunci na tsarkake dukkanin masu aikata zina da matan aure tare da wanke su tatas.
Wannan itace sabuwar doka ta biyu mai cike da ban mamaki makamanciyar ta rayuwar Mutanen farko da aka zartar kan al'ummar kasar ta Indiya, inda a ranar 6 ga watan Satumba kotun kolu ta kasar ta halarta luwadi kamar yadda ta kasance a shekarar 1861.
A yayin murnar wannan sabon hukunci, kotun ta bayyana cewa a baya can sashe na 377 cikin dokokin kasar Indiya ya zamto abin muzantawa ga masu aikata Luwadi inda a halin yanzu aka halarta hakan da kuma Zina da matan aure ba tare da wani hukunci ba.

Asali: UGC
Rahotanni sun bayyana cewa, shekaru kimanin ashirin da suka gabata akwai hukuncin dauri na shekaru biyar da zama a gidan kaso ga duk wanda ya kwanta da Matar aure ba tare da amincewar mijinta ba.
KARANTA KUMA: Ni zan kasance shugaban Kasar Najeriya a 2019 - Kwankwaso
Sai dai wani fitaccen dan kasuwa na kasar ya kalubalanci wannan kotu dangane da wannan lamari, inda ya nemi akan ta soke wannan mummunar doka da a cewar sa cin mutunci ne gami da wulakantaswa da kuma cin zarafin Matan aure.
Cikin zayyana dalilan ta, kotun ta bayyana cewa wannan sabon hukunci zai bai wa mata dama da kuma 'yancin na samun zabin Mutumin da suke da sha'awar kwanciya da shi a duk lokacin da suka bukata ba tare da wani muzguni daga bangaren Mazajen su ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng