Allah ya kyauta: Matar aure da take zuwa tayi lalata da kato a titi ta rasa ranta a wajen zubar da cikin shege

Allah ya kyauta: Matar aure da take zuwa tayi lalata da kato a titi ta rasa ranta a wajen zubar da cikin shege

- Wata matar aure da ke da 'ya'ya hudu ta rasa ranta a garin zubar da cikin shege

- Matar wacce aka gano tana zuwa ta kwanta da wani saurayi dan shekara 25 ta mutu ne bayan ciki ya shiga tsakaninta da saurayin nata

- Bayan mijinta ya garzaya da ita asibiti likita ya bayyana masa cewa ta sha maganin zubar da ciki ne wanda kuma ya lalata mata mahaifa

Wata mata mai 'ya'ya guda hudu wacce aka bayyana sunanta da Mrs Chinasa Odah, an bayyana mutuwar ta bayan taje zubar da cikin shege, wanda ya saka ta yi ta zubar da jini.

Matar da take 'yar asalin garin Inikiri Effum dake karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi ta mutu a ranar 24 ga watan Agustan na, a wani asibiti bayan ta sha maganin da zai zubar mata da ciki.

Matar mai shekaru 29 ta samu cikin ne sanadiyyar dagantakar dake tsakaninta da wani matashin saurayi mai shekaru 25 wanda aka bayyana sunan shi da Monday Mgbada.

KU KARANTA: Abu dai sai gaba yake yi: Aisha Idris ta sake cin mutuncin Ali Nuhu da yaransa inda ta yi musu tatas

An gano wannan cin amana da matar auren take yi bayan mijinta Micheal Odah ya garzaya da ita asibiti, inda likita ya tabbatar mishi da cewa ta sha maganin zubar da ciki ne.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar 'yan sanda sun cafke Mgabada bayan matar ta bayyana cewa shine ya tilasta tasha maganin zubar da cikin, wanda yayi sanadiyyar lalacewar mahaifarta.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Loveth Odah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa kuma sun kama Mgbada, kuma ana gabatar da bincike akan lamarin

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel