An Gano Abin da zai Jefa 'Yan Najeriya Miliyan 13 a Talauci a 2025, an Gargadi Gwamnati
- Rahoton PricewaterhouseCoopers International Limited (PwC) ya nuna cewa hauhawar farashi, tsadar rancen kuɗi, da faɗuwar darajar Naira za su jefa mutane miliyan 13 cikin talauci
- A cewar Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS), hauhawar farashi ya kai kaso 34.80 cikin ɗari a Disambar 2024, wanda ya shafi tattalin arziki da rayuwar jama'a
- PwC ta gargadi gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tattalin arziki, tare da hana ƙarin mutane shiga talauci mai tsanani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Bincike ya bayyana cewa akalla mutane miliyan 13 a Najeriya za su shiga matsanancin talauci a wannan shekara ta 2025 da muke ciki.
Wannan na kunshe a sabon rahoto mai suna ‘Kasafin Kuɗi da Yanayin Tattalin Arzikin Najeriya na 2025’, wanda kamfanin PricewaterhouseCoopers International Limited (PwC) ya fitar.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa hauhawar farashin kayayyaki, tsadar rancen kuɗi, da kuma faɗuwar darajar Naira za su sa ƙarin ‘yan Najeriya shiga cikin tsananin talauci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan karuwar talauci a Najeriya
Rahoton PwC ya nuna cewa duk da ikirarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa tattalin arzikin ƙasar yana inganta, akwai yiwuwar yawan masu fama da talauci zai ƙaru nan da shekarar 2025.
PwC ta ce:
“Adadin mutanen da ke rayuwa ƙarƙashin layin talauci na ƙasa zai ƙaru da kimanin mutane miliyan 13 nan da shekarar 2025,” inda ta danganta wannan ƙaruwa da matsalar hauhawar farashi da tsadar rayuwa a ƙasar.
Najeriya ta fuskanci hauhawar farashi
A cewar Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS), adadin hauhawar farashi a Najeriya ya kai 34.80% a watan Disambar 2024.
Haka zalika, Shugaban Ƙungiyar Masu Sarrafa Kayayyaki ta Najeriya (MAN), Cif Francis Meshioye, ya ce sun fuskanci hauhawar farashi.
Ya kara da cewa sun shiga matsaloli da su ka samo asali daga matsalolin tattalin arziki kamar hauhawar farashi, tsadar rancen kuɗi, da faɗuwar darajar Naira.
Rahoton PwC ya gargadi Najeriya
Rahoton da PricewaterhouseCoopers International Limited (PwC) ya gargadi mahukunta a Najeriya da su dauki matakan gaggawa domin inganta tattalin arziki.
Rahoton ya jaddada cewa idan ba a ɗauki matakai masu inganci ba, tattalin arzikin ƙasar zai ci gaba da fuskantar matsaloli, tare da ƙara jefa miliyoyin ‘yan ƙasa cikin talauci mai tsanani.
An ragargaji Tinubu a kan hauhawar farashi
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mai ba da shawara kan harkokin noma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dolapo Bright, ya yi suka kan matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka.
Mista Bright ya bayyana janye haraji kan kayan abinci da ake shigo da su, inda ya kara da cewa cewa hauhawar farashin man fetur da dizil, waɗanda ake amfani da su wajen sufuri da noma ya kara hauhawar farashi.
Tsohon hadimin ya yi kira ga gwamnati da ta samar da yanayi mai kyau ga manoma domin bunkasa tattalin arziki a Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng

