China na Gina Kamfanin $200m a Nasarawa, za a Biya Ma'aikata N500,000
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ziyarci hedikwatar Jiuling Lithium a kasar China domin tabbatar da ci gaban ginin kamfanin da yake ginawa
- Kamfanin Jiuling Lithium zai gina masana’anta mai iya sarrafa tan miliyan 6 na lithium cikin watanni 18 a Nasarawa, tare da daukar ma’aikata da yawa
- Canmax Lithium ya yi alkawarin biyan albashin da ya zarce mafi karancin albashin Najeriya na N70,000, har zuwa N500,000 ga ma’aikatan kamfanin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
China - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kai ziyara kasar China domin neman ci gaban da ginin masana’antar da kamfanin Jiuling Lithium ke ginawa.
Wannan ziyara ta kasance wani bangare na shirin gwamnati na jawo zuba hannun jari daga ketare domin habaka tattalin arzikin jihar.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Source: Facebook
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana yadda suke tattaunawa da jami'an kamfanin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A lokacin ziyarar, gwamnan ya samu damar ganin aiki da kuma yadda kamfanin Jiuling Lithium ke gudanar da ayyukansa, wanda ke shirin kafa wata babbar masana’anta a jiharsa.
An bayyana cewa masana’antar za ta zama wata babbar hanya ta samar da ayyukan yi ga al’ummar jihar.
Alkawuran kamfanin China ga Nasarawa
Kamfanin Jiuling Lithium, wanda ke sarrafa albarkatun kasa domin samar da batir ya bayyana gamsuwarsa da yanayin kasuwanci mai kyau a jihar Nasarawa.
A cewar kakakin kamfanin;
“Yanayin kasuwanci a Nasarawa yana da kyau sosai, hakan ya sa muka yanke shawarar zuba jari mai tsoka a jihar.”
Gwamna Sule ya tabbatar da kudurin kamfanin na kammala aikin masana’antar cikin watanni 18, wanda hakan zai ba da damar samar da ayyuka ga dubban matasa a jihar.

Kara karanta wannan
Jigawa: Gwamna zai ciyar da mabukata 189, 000 a Ramadan, an ji kudin da zai kashe
Za a biya ma'aikata albashi N500,000
A yayin wata ziyara daban zuwa kamfanin Canmax Lithium, Gwamna Sule ya tattauna da shugabannin kamfanin kan yadda al’ummar jihar za su amfana da su.
Shugabannin Canmax Lithium sun ce mafi yawan ma’aikatan kamfaninsu za su fito daga Nasarawa, kuma za su ba da albashin da ya zarce mafi karancin albashin Najeriya.
“Za mu ba ma’aikata albashi mai tsoka wanda zai kai har Naira 500,000 ga ma’aikata masu matsakaicin matsayi,”
Ana ganin cewa mataki zai kara wa jihar Nasarawa daraja da kuma rage yawan zaman banza ciki al'ummarta.

Source: Facebook
Karfafa zuba jari a jihar Nasarawa
Wannan ziyara ta Gwamna Sule zuwa kasar China wani mataki ne na tabbatar da cikar burinsa na ganin an samu cigaban tattalin arziki mai dorewa a Jihar Nasarawa.
Kamfanonin Jiuling Lithium, Avatar, da Ganfeng Lithium sun kasance cikin wadanda suka zuba jari a jihar domin samar da kayan aikin zamani da ake bukata wajen cigaban tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
Gwamnan ya nuna matukar farin cikinsa kan yadda kamfanonin ke nuna kwarewa da sadaukarwa wajen samar da abin da zai taimaka wajen bunkasa rayuwar al’ummar jihar.
Za a yi noman zamani a Nasarawa
A wani labarin, mun ruwaito muku cewa gwamnan jihar Nasarawa ya fara shirin hadaka da wani kamfanin China a kan noma.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana aniyarsa ta ganin cewa an noma dukkan filayen jihar tare da yin amfani da kayayyakin noma na zamani.
Asali: Legit.ng