Gwamnatin Tinubu Ta Haramta Kungiyar Lakurawa, Ta Fadi Hukuncin Masu Goyon Bayanta

Gwamnatin Tinubu Ta Haramta Kungiyar Lakurawa, Ta Fadi Hukuncin Masu Goyon Bayanta

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ayyana kungiyar Lakurawa a matsayin ta ta'addanci tare da haramta ta da sauran kungiyoyin da ke da alaka da ita
  • Alkalin kotun, Mai Shari’a, James Omotosho, ya bayar da umarnin ne bisa bukatar Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, cikin wata karar gaggawa
  • Kotun ta ce ayyukan kungiyar Lakurawa sun haɗa da satar shanu, garkuwa da mutane, kai hari, da yada ra’ayoyin da ke barazana ga tsaron ƙasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta haramta ayyukan kungiyar Lakurawa a yau Alhamis 23 ga watan Janairun 2025.

Wannan hukunci ya shafi sauran kungiyoyin da ke yankin Arewacin Najeriya musamman Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Gwamnatin Najeriya ta haramta ayyukan kungiyar Lakurawa
Gwamnatin Bola Tinubu ta ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin yan ta'adda. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yadda sojoji suka shirya kakkabe kungiyar Lakurawa

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Mai Shari’a James Omotosho ya yanke hukuncin ne bayan an gabatar da karar gaggawa daga Ministan Shari’a, Mr. Lateef Fagbemi, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da Rundunar sojojin Najeriya ta ƙaddamar da babban aikin kawar da Lukurawa, sabuwar ƙungiyar ta’addanci da ta bayyana.

Sabuwar ƙungiyar ta sami damar shigowa Najeriya ne ta hanyar haɗin gwiwa da mayaƙan jihadi daga Mali, Libya da kuma Nijar.

An ce Lakurawa ta haɗa kai da ’yan bindigar gida, inda take jan hankalin matasa tare da shirin fadada ayyukanta na ta’addanci.

Kotu ta ayyana Lakurawa a matsayin yan ta'adda

Ministan ya bukaci kotu da ta bayar da umarni hudu, ciki har da ayyana Lakurawa a matsayin kungiyar ta’addanci bisa dokar hana ta’addanci ta kasa.

Darakta a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, Mista David Kaswe ya gabatar da takardar karar da aka shigar ranar 14 ga watan Janairun 2025.

Jami’i a sashen karar ma’aikatar, Michael Akawu, ya ce kungiyar Lakurawa ta aikata laifukan ta’addanci kamar sata, garkuwa da mutane da kai hare-hare.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gamu da matsala: Kotun Kano ta yi hukunci kan kama Muhuyi Magaji

Hukuncin da ke jiran masu goyon bayan Lakurawa

Kotun ta ce ayyukan Lakurawa sun haddasa mutuwar mutane, asarar dukiya, da barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa, don haka ta cancanci a haramta ta, cewar rahoton Daily Nigerian.

Mai Shari’a Omotosho ya bayar da umarni na haramta kungiyar Lakurawa da duk kungiyoyin da ke da manufa irin tasu, musamman a Arewa maso Yamma da Tsakiya.

Ya ce duk wanda ya shiga ko goyi bayan ayyukansu, a ko wace hanya, za a dauki matakin shari’a a kansa bisa wannan hukunci.

Irin ta'addancin da Lakurawa ke yi

Kun ji cewa hukumomin Najeriya sun tabbatar da samuwar sabuwar kungiyar yan ta'addan Lakurawa a wasu sassa na Sokoto da Kebbi.

Mazauna wuraren da yan ta'addar ke zama sun bayyana yadda suka fara muzgunawa al'umma da ta'addancin da suke yi.

An kuma bayyana cewa yan ta'addar suna amfani da yare da dama wajen yin magana; Fulatanci, Kanuri, Turanci da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.