Bidiyon Gonar Tabar Wiwi da NDLEA Ta Gano a Jihar Kano, Wani Dattijo Ya Shiga Hannu

Bidiyon Gonar Tabar Wiwi da NDLEA Ta Gano a Jihar Kano, Wani Dattijo Ya Shiga Hannu

  • Hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a jihar Kano ta cafke wani Malam Sabo da ke noma tabar wiwi a cikin gonarsa
  • Malam Sabo ya shaidawa hukumar NDLEA cewa shi yana noma wiwin ne domin ya sha ba wai don ya rika sayarwa ba
  • A cikin bidiyon da hukumar NDLEA ta fitar, an ga dami damin shukar wiwi yayin da Malam Sabo ya ba da labarin yadda aka kama shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) reshen jihar Kano ta gano wata gona da ake noma tabar wiwi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da NDLEA ke gano gonar wiwi a Kano ba, amma wannan karon an kama wani dattijo ne matsayin mai gonar.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Malam Sabo ya yi bayanin yadda hukumar NDLEA ta kama shi a cikin gonarsa ta wiwi
Hukumar NDLEA ta kama wani Malam Sabo da ke noma tabar wiwi a jihar Kano. Hoto: NDLEA
Asali: Facebook

Mai magana da yawun NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya wallafa bidiyon hirar da suka yi da dattijon bayan kama shi a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLEA ta kai samame gonar wiwi a Kano

A cikin biiyon, an ga dattijon mai suna Sabo a gaban gonarsa, wacce ke dauke da tushe-tushe na bishiyar wiwi, wadda har ta fara bin bango.

A cikin hirar da aka yi da Malam Sabo, an shekara 50, an tambaye shi ko wacce iriyar ciyawa ce ake gani a bayansa, sai cewa ya yi:

"Wannan tabar wiwi ce."

A labarin da Sabo ya bayar, ya ce yana cikin gonar tasa sai ya ga wasu mutane sun karaso wajen, wadanda ya ce ya fahimci "ma'aikata ne.

Dattijo na noma wiwi a gonar karas

Dattijon ya shaidawa cewa jami'an sun kama shi da suka gano cewa wiwi yake nomawa tare da karas, domin ya yi basaja.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

Sai dai yayin da NDLEA ke tuhumarsa, dattijon ya dage kan cewa shi ba nomata yake yi ba don ya sayar, yana noma wiwin ne domin amfanin kansa.

"Ni ina nomawa ne don na sha. Amma dai dan kwana biyu ko hudu ina sayar da 'yar ta dubu daya zuwa dubu biyu haka."

- A cewar dattijon.

Da aka tambaye shi ko ya san cewa noma wiwi laifi ne, Malam Sabo ya ce kwarai ya sani amma tsautsayi ne ya sanya shi noma ta.

Malam Sabo dai ya yi addu'a a kan Allah ya shiryi masu yin iri nasa, yayin da hukumar NDLEA ta tabbatar da cewa yana sayar da tabar wiwin.

Kalli bidiyon a kasa:

NDLEA ta gano tafkekekiyar gonar wiwi

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NDLEA ta sanar da cewa ta gano wata tafkekekiyar gona da ake noma tabar wiwi a jihar Kano.

Shugaban hukumar NDLEA reshen jihar Kano, Malam Isah Limita (2021) ya tabbatar da gano gonar da suka yi a garin Gwarzo.

Malam Isah ya bukaci jama'a da su taimakawa hukumar da bayanan sirri ta yadda zasu kama tare da hukunta masu sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.