Babbar magana: An gano eka 11,000 ta gonar wiwi a wannan jihar ta Najeriya

Babbar magana: An gano eka 11,000 ta gonar wiwi a wannan jihar ta Najeriya

Kwamandan hukumar rundunar nan dake yake da safara tare kuma da shan miyagun kwayoyi ta tarayyar Najeriya watau National Dr*g Law Enforcement Agency, NDLEA a jihar Ondo mai suna Muhammad Sokoto ya sanar da samun nasarar bankado gonar wiwi mai girman eka 11,000.

Kamar dai yadda muka samu, Kwamandan rundunar a jihar ta Ondo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya ya kuma ce tuni dai hukumar ta lalata wannan gonar a tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2018.

Babbar magana: An gano eka 11,000 ta gonar wiwi a wannan jihar ta Najeriya
Babbar magana: An gano eka 11,000 ta gonar wiwi a wannan jihar ta Najeriya

KU KARANTA: Jahohi 35 da za su fuskanci ambaliyar ruwa

A wani labarin kuma, Jami'an hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da safarar mutane zuwa kasashen ketare watau National Agency for the Prohibition of Trafficking in Persons, watau NAPTIP a takaice sun sanar da samun nasarar cafke wasu mutane biyu da laifin safarar 'yan mata zuwa karuwanci a Saudiyya.

Mutanen biyu wadanda dukkan su daraktoci ne na wani kamfanin jigilar mahajjata ne a garin Abuja masu suna Ibrahim Wali da kuma Nasiru Jubril a zarge su ne da kai 'yan mata daga Arewa har su 96 Saudiyya amma har yanzu basu dado da su ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng