An Jefa Limamin Masallaci a Tashin Hankali, Ya La'anci Wadanda Suka Kashe Iyalansa

An Jefa Limamin Masallaci a Tashin Hankali, Ya La'anci Wadanda Suka Kashe Iyalansa

  • Wani malamin addinin Musulunci a jihar Ondo ya saukar da ruwan tsinuwa da addu'ar masifa ga mutanen da suka kashe iyalansa
  • Rahoto ya nuna cewa wasu 'yan kungiyar asiri ne suka kashe matar malamin da dansa a garin Owo a wani rikicin kungiyoyin
  • Alhaji Abdulkareem Adedokun ya kwashewa wadanda suka kashe iyalansa albarka, tare da cewa babu wanda zai iya warware hakan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Wani limami a garin Owo da ke jihar Ondo, Alhaji Abdulkareem Adedokun ya yi ruwan kalaman la'ana ga makasan iyalansa.

An rahoto cewa rikici tsakanin 'yan kungiyoyin asiri ya barke a garin na Owo, wanda ya kai ga kashe matar limamin da dansa.

Malamin addini a Ondo ya yi tsinuwa da aka kashe matarsa da dansa
Limamin masallaci a Ondo ya yi tsinuwa da aka kashe matarsa da dansa a rikicin kungiyar asiri. Hoto: Adedokun Abdulkareem
Asali: Facebook

An kashe mata da dan wani limamin Ondo

Rahoton Punch ya nuna cewa an kashe matar Alhaji Abdulkareem mai suna Temitope Adedokun da dansa mai suna Abdulmalik Adedokun.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce dai wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar 6 ga watan Janairun 2025, kuma mutane hudu ne aka kashe a rikicin.

A yayin artabu tsakanin 'yan kungiyar asirin, matar limamin da dansa suka gamu da ajalinsu, lamarin da ya yi matukar daga hankalin malamin addinin.

A wani mataki na kwantar da tarzoma, gwamnatin jihar Ondo ta sanya dokar hana fita a garin daga safiya zuwa dare yayin da 'yan sanda suka kama mutane 19.

Limami ya fusata da kashe mata da dansa

A sakon tsinuwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, limamin masallacin ya nuna matukar takaici da bacin ransa, tare da bayyana yadda aka kashe iyalan nasa.

A cewar malamin, sakon nasa budaddiyar wasika ce ga mutanen karamar hukumar Owo a jihar Ondo da ke gida da waje da kuma daukacin jama'a kan kashe iyalansa.

A cikin wasikar, limamin ya ce:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

"Ni Liman Alhaji Abdulkareem Adedokun, ina amfani da wannan damar domin sanar da jama'a cewa 'yan kungiyar asiri sun kashe matata Temitope Adedokun.
"Kuma sun kashe dana, Abdulmalik Adedokun a ranar 6 ga watan Janairun 2025 yayin da suka farmakin shagon matata."

Malami ya yi ruwan tsinuwa ga makasan iyalansa

Malamin addinin ya ci gaba da cewa:

"Abin takaicin shi ne yadda wasu 'yan siyasa suka siyasantar da kisan matata da dana, duk da cewa sun san cewa babu wani a zuriyar Adedokun da ke harkar tsafi.
"Bisa ga turbar kakana, Almustapha Adedeji Jika Anabi, wanda ya kawo Musulunci a garin Owo da wasu sassan Ondo, ina la'antar wadanda suka kashe Temitope Adedokun and Abdulmalik Adedokun.
"Ina rokon Allah ya tsine tare da saukar da masifa a kan kungiyar asirin da ta yi aika aikar da iyalansu, da masu goyon bayansu da 'yan siyasa da sarakuna da duk jami'an tsaro da iyalansu da ke goyon bayansu.

Kara karanta wannan

Yan Siyasar Kano da ke kokarin sulhunta Kwankwaso da Ganduje

"Daga rana irin ta yau, duk wani yaro da aka haifa a zuriyar wadannan tsinannun zai yi mutuwar wulakanci idan suka kai shekarun Abdulmalik dina da suka kashe
"Daga yanzu har tashin alkiyama, babu wanda zai iya karya wannan tsinuwar har sai idan za su iya dawo mun da rayuwar dana Abdulmalik."

'Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani malamin Musulunci a jihar Gombe mai suna Abubakar Mushawy Ibrahim.

An ce masu garkuwa sun sace malamin tare da matarsa da yaransa biyu kuma daya daga cikin yaran jariri ne dan kwana daya da haihuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.