Yadda Lokutan Salla ke Canjawa a Najeriya da Mafita ga Musulmi
- Malamai suna bayani kan cewa yin salla kafin lokacinta bai halatta ba, kamar yadda suka ce Allah ya shar’anta gabatar da salloli ne a kan lokaci
- A cewar wani masani a harkokin ganin wata, Simwal Usman Jibril, ana yawan yin sallar La’asar kafin lokaci a Najeriya, musamman tsakanin Janairu da Maris
- An shawarci jama’a su dinga amfani da tsarin zamani na kalanda ko manhajojin wayar salula domin tabbatar da suna yin sallah a kan lokaci
- Wani ladani a jihar Gombe, Malam Adamu Awak ya zantawa Legit hanyar da ya ke bi wajen lura da lokutan salla a masallacinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Malamai sun bayyana cewa daya daga cikin muhimman sharuddan karɓuwar sallah shi ne a tabbatar da cewa an yi ta a lokacin da aka shar’anta.
Haka zalika suna gargadi da cewa duk wata sallah da aka yi kafin lokacinta ta sabawa shari’a kuma ba za ta karɓu ba.

Asali: Twitter
A wata sanarwa mamba a kwamitin ganin wata na kasa, Simwal Usman Jibril ya wallafa a X, ya yi kira ga jama’a kan muhimmancin tabbatar da lokutan sallah kafin gudanar da ibadar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta jaddada cewa yawan yin sallar La’asar kafin lokaci ya yi yawa a Najeriya musamman saboda yadda aka saba da amfani da lokuta ba tare da duba canjin yanayi ba.
Lokutan da sallar la’asar ke fara shiga
A cewar Simwal, shari'a ta bayyana cewa lokaci mafi dacewa na fara sallar La’asar shi ne lokacin da tsawon inuwar wani abu ya kai tsawonsa a lokacin da rana ta ke tsakiyan sama.
Simwal Usman Jibril ya bayyana cewa daga tsakiyar watan Janairu zuwa farkon watan Maris, tsawon inuwa a wurare da dama a Najeriya yakan fi tsayi har ma kafin lokaci ya cika.
Hakan yana sa wasu su yi La’asar kafin lokacinta. Haka zalika, irin wannan matsala na faruwa daga tsakiyar watan Yuni zuwa watan Yuli.
Matsalar sabawa lokutan sallah
A yayin da lokutan sallar Magriba suke da sauƙin lura saboda ana gani lokacin faduwar rana, lokacin La’asar yana bukatar kulawa ta musamman saboda ba kowa ke lura da yanayin inuwa ba.
A cewar Simwal, sau da yawa, mutane na amfani da jadawalin da aka saba amfani da shi na lokutan sallah ba tare da yin la’akari da canjin yanayi ba.
Wannan yana nufin cewa jama’a na yin kuskure wajen gudanar da wannan ibada mai muhimmanci.
Shawarwarin amfani da fasaha
Simwal Usman Jibril ya bukaci Musulmi da su rika amfani da fasahar zamani kamar kalandar Musulunci da manhajojin wayar salula domin tabbatar da cewa suna yin sallah a lokacinta.
"Saboda haka, ba za mu iya cewa ba mu da uzuri ba yayin da muke da kayan aikin zamani da za su taimaka mana wajen gano lokutan ibada.”

Kara karanta wannan
Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su
- Simwal Usman Jibril
An kuma yi kira ga masu kula da masallatai da su tabbatar da cewa suna yin amfani da sababbin kalanda da ake rubuta lokutan sallah kamar yadda ya dace da yanayi na kowanne lokaci.
Legit ta zanta da ladani a Gombe
Wani ladani a jihar Gombe, Malam Adamu Awak ya ce duk da shekaru san ja sosai, yana kokarin kiyaye lokutan salla.
Ladanin ya ce;
"Ina amfani da lokutan salla da kungiyar Izala ke rabawa duk wata, amma idan bai samu da wuri ba ina tambayar matasa masu manyar wayoyi ko an samu sauyin lokaci."
Malamin jami'a ya haddace Kur'ani
A wani rahoton, kun ji cewa wani malami a jami'ar Legas ya kafa tarihin haddace Kur'ani yana mai shekaru 59.
Legit ta wallafa cewa Farfesa Tajudden Yusuf ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su riki karatun Kur'ani da kuma fahimtar ma'anoninsa.
Asali: Legit.ng