Karin Kudin Kira: NLC za Ta Saka Kafar Wando Daya da Gwamnatin Tinubu
- NLC ta bayyana cewa karin 50% na kudin kira ba zai yiwu ba a lokacin da ma’aikata da talakawa ke fama da matsanancin talauci
- Shugaban NLC ya zargi gwamnatin tarayya da fifita ribar manyan kamfanoni fiye da jin dadin talakawan da ta ke jagoranta
- NLC ta yi kira ga gwamnati, NCC, da majalisar kasa da su dakatar da wannan karin kudin kira domin ba wa jama’a damar tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ta soki karin kudin kira da gwamnatin tarayya ta amince da shi, inda ta bayyana shi a matsayin hari ga jin dadin ma’aikata da talakawa.
A ranar Litinin, hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince wa kamfanonin sadarwa da su kara kudin kira da 50% na abin da su ke caji a baya.

Asali: Facebook
The Cable ta wallafa cewa Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce wannan matakin ya nuna rashin kulawa ga jin dadin al’ummar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NLC ta soki karin kudin kira
Nigerian Tribune ta wallafa cewa Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi kuskure wajen amincewa da karin kudin kira.
Ya kara da cewa halin da 'yan Najeriya su ke ciki a yanzu ba na jin dadi ba ne, ganin yadda su ke fama da matsanancin matsin tattalin arziki.
Ajaero ya ce:
“Wannan matakin, da aka dauka a irin wannan lokaci da ma’aikata da talakawa ke fama da wahalhalun tattalin arziki, ya zama wani hari ga jin dadin su da kuma barin jama’a ga kamfanonin kasuwanci masu son riba kawai."
"Ana bukatar saukin kiran waya," NLC
Kungiyar kwadago ta bayyana cewa talakawan Najeriya na bukatar samun kiran waya cikin sauki saboda muhimmancinsa ga rayuwarsu ta yau da kullum.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Kungiyar ta ce:
“Talaka mai samun mafi karancin albashi na N70,000 a wata yana kashe kusan 10% a kan sadarwa. Wannan karin zai ninka abin da yake kashewa daga N7,000 zuwa N10,500 a wata, wanda ya kai kusan 15% na albashinsa—wannan tsadar ba za a iya jurewa ba.”
Kungiyar ta yi zargin cewa wannan karin ya nuna yadda gwamnati ta fi fifita ribar manyan kamfanoni fiye da jin dadin talakawa.
Gwamnati ta ba NLC mamaki
Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero, ya bayyana mamakin yadda gwamnatin tarayya ta amince da karin 50% na kudin kiran waya cikin wata daya.
Ya ce:
“Wannan bambancin yana nuna cewa gwamnati ta fi karkata wajen goyon bayan kamfanoni masu arziki fiye da jin dadin ma’aikata da talakawan da suke cikin al’umma. Ya kamata mu tambaya: Yaushe ne gwamnati za ta tsaya tsayin daka wajen kare mutanen da ta rantse za ta yi wa hidima?”
Kungiyar NLC ba ta kin karshin kudin kira
Ajaero ya bayyana cewa kungiyar kwadago ba ta kin yin sake duba farashin kira ba, amma ba ta goyon bayan karin da aka yi na 50%, ta yi barzanar daukar matakin zanga-zanga.
Ya ce:
“Don haka, muna kira ga gwamnati, NCC, da majalisar kasa da su dakatar da aiwatar da wannan karin farashi da ba a yi tunani sosai ba domin ba wa jama’a damar tattaunawa a kai.”
NLC ta fusata a kan karin kudin fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta kasa ta yi tir da ƙarin farashin man fetur zuwa tsakanin N1,050 da N1,150, wanda ta bayyana a matsayin rashin tausayin talaka.
a zargi masu sayar da man fetur da amfani da wannan damar wajen ƙara farashi domin cin kazamar riba, tana mai kiran su makiyan talakawa da ke gallazawa ma'aikatan Najeriya.
Asali: Legit.ng