Matasa Sun Sake Zuwa Diban Fetur da Tanka Ta Fadi, Yan Kasuwa Sun Tsere
- An sake samun iftila'in faduwar tankar man fetur a birnin Jalingo da ke jihar Taraba a yau Laraba 22 ga Janairun 2025
- Matasa sun taru a wurin hatsarin tankar man yayin da jami'an tsaro suka dakatar da su daga diba saboda hatsarin da ke ciki
- Hukumar NSCDC da 'yan sanda sun dauki matakai don kare rayuka da dukiyoyi, yayin da 'yan kasuwa suka rufe shagunansu saboda fargaba
- An tabbatar direban tankar ya samu rauni inda aka garzaya da shi asibiti, yayin da jami'ai suka tabbatar da tsaron yankin Mile 6
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jalingo, Taraba - Kwanaki kadan bayan kusan mutum 100 sun rasa rayukansu a hatsarin tankar mai a Jihar Neja, an sake samun matsala a Taraba.
Wasu matasa sun taru a wurin hatsarin tankar mai a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba a yau Laraba 22 ga watan Janairun 2025.

Asali: Original
Yadda rayuka suka salwanta a jihar Niger
Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Taraba, SP Abdullahi Usman ya tabbatar da faruwar wannan lamari, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan an tabbatar da mutuwar mutane fiye da 100, ciki har da wata mata mai juna biyu sakamakon fashewar tankar mai a Dikko Junction a jihar Neja.
A farko tankar ta zubar da mai, lamarin da ya ja mutane suka taru don diban man fetur, wanda daga bisani mummunan gobara ta tashi a wurin.
Duk da babu wata sanarwa a hukumance amma rahotanni sun nuna cewa jami'an hukumar kwana-kwana sun duƙufa aikin kashe gobarar.
Wata tankar mai ta kuma faduwa a Taraba
Rahotanni suka ce an gano matasan na debo man fetur daga cikin tankar mai da ta samu matsala kafin jami'an tsaro su isa.
Jami'an NSCDC da 'yan sanda sun dakatar da matasan a yankin Mile 6 da ke Jalingo, inda tankar ta kife tare da zubar da mai.
A lokacin wannan lamari, 'yan kasuwa dake kusa da wurin sun rufe shagunansu tare da tserewa don kaucewa hatsari ko asara.
Jami'an tsaro sun kawo daukin gaggawa kan lamarin
Mai magana da yawun hukumar NSCDC a Taraba, Mista Illia Samuel, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya tabbatar da cewa direban tankar ya ji rauni, an garzaya da shi asibiti don samun taimako.
Mista Samuel ya bayyana cewa sun tura jami'ansu cikin gaggawa don hana tashin wani hatsari da ka iya yin barna ga mazauna yankin da matafiya.
Buhari ya jajanta kan iftila'in jihar Niger
A baya, kun ji cewa Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana kan iftila'in fashewar tankar mai da ya faru a jihar Niger.
Buhari ya nuna takaicin rashin jin gargadin hukumomi da mutane ke yi game da haɗarin ɗaukar man fetur daga tankar da ta fashe.
Tsohon shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da Gwamnatin Neja bisa tashin hankalin fashewar tankar mai a kwanar Dikko.
Asali: Legit.ng