"Dare Ɗaya Allah Kan Yi Bature": Gwamna Abba Ya Canza Rayuwar Wata Makauniya a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba da jajircewar Hassana Nazifi Shehu, wata mai lalurar makanta da ta kammala digiri a jami'ar BUK da ke Kano
- Abba ya ba da umarnin ɗaukarta aiki nan take kuma ya yi alƙawarin naɗa ta a hukumar kula da haƙkokin naƙasassu da zai kafa nan gaba
- Gwamnan ya yi haka ne domin karfafa guiwar naƙasassu wajen tunkarar duk wani kalubale na rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin ɗaukar Hassana Nazifi Shehu Minjibir, wata matashiya mai nakasar gani aikin gwamnati.
Hassana, wacce Allah ya jarabta da rashin gani watau makanta ta kammala karatun digirinta a Jami’ar Bayero, Kano (BUK).

Asali: Facebook
Gwamna Abba Gida Gida ya ɗauki makauniya aiki
Umarnin ɗaukar makauniyar aiki na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya ɗauke ta aiki ne kai tsaye saboda gamsuwa da kwazonta da jajircewarta duk da kalubalen da ta fuskanta wajen neman ilimi.
Hassana Minjibir, wadda ta kammala digirinta a fannin ilimi na musamman, ta ja hankalin gwamnan yayin wani taron tallafawa mata da aka shirya a jihar Kano.
A wannan taron, Hassana ta bayyana yadda ta sha gwagwarmayar neman ilimi duk da ba ta gani, abin da ya burge gwamnan sosai.
Gwamnan jihar Kano ya yabawa makauniyar
Gwamna Abba ya bayyana cewa irin wannan jarumta da jajircewa ya dace a yaba kuma a tallafa mata.
A cikin jawabin gwamnan, ya ce Hassana Minjibir ta zama abin koyi ga sauran matasa, musamman wadanda suke fuskantar kalubale a rayuwa.
Ya yabawa irin kwazon da ta nuna wajen samun ilimi da kuma yadda ta ci gaba da kasancewa mai dogaro da kanta duk da halin da take ciki.
Abba ya yi alkawarin naɗa ta a hukumar PWD
Baya ga bai wa Hassana aiki a gwamnatinsa, Gwamna Abba ya kuma yi alkawarin nada ta a hukumar kula da hakkokin masu nakasa (PWD), wadda za a kafa nan gaba kadan a Kano.
Wannan alkawari ya nuna kudirin gwamnan na ganin an ba mutane masu nakasa dama a cikin al’umma tare da tabbatar da cewa an kare hakkokinsu.
Haka kuma, gwamnan ya umarci shugaban ma’aikatan jihar Kano da ya gaggauta ba Hassana takardar shaidar ɗaukar aikin gwamnati ba tare da wani bata lokaci ba.
Wannan matakin ya nuna irin jajircewar gwamnan wajen tabbatar da cewa gwamnati ta tallafa wa masu nakasa domin su ba da gudummuwa a cikin al’umma.
Hassana Nazifi Shehu Minjibir ta zama abin alfahari ga jihar Kano, kuma wannan tallafi da gwamnan ya ba ta zai kasance alamar goyon baya ga sauran mutane masu nakasa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Gwamnan Kano zai karasa ayyukan Kwankwaso
Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya ƙwace wasu filaye da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban APC na yanzu, Dr. Abdullahu Umar Ganduje ya raba.
Abba Gida-Gida ya ɗauki wannan matakin ne domin ƙarasa wasu ayyuka da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya faro a Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng