"Ku Yi Hattara": Gwamnatin Sokoto Ta Ankarar da Jama'a kan Sabuwar Barazanar 'Yan Ta'adda

"Ku Yi Hattara": Gwamnatin Sokoto Ta Ankarar da Jama'a kan Sabuwar Barazanar 'Yan Ta'adda

  • Gwamnatin Sokoto ta bayyana nasarorin da jami'an tsaro suke samu kan ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar gaba a gabashin jihar
  • Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, ya buƙaci jama'a da su sanyo ido kan ƴan ta'addan da ke tserewa daga ragargazar sojoji
  • A cikin sanarwar da ya fitar, ya kuma buƙaci mutanen gabashin Sokoto da su kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba ga jami'an tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jiihar Sokoto ta gargadi mazauna yankin gabashin jihar da su kasance masu taka tsantsan game da ƴan ta’addan da ke guduwa.

Gwamnatin ta yi wannan tunatarwar ne biyo bayan ci gaba da kai hare-hare da sojoji suke yi kan ƴan ta’adda a gabashin Sokoto da kewaye.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

Gwamnatin Sokoto ta yi gargadi kan 'yan ta'adda
Gwamnatin Sokoto ta bukaci jama'a su kara sanya ido kan 'yan ta'adda Hoto: @AhmedAliyuskt
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), wanda kuma aka fi sani da Sadaukin Gwadabawa, ya sanyawa hannu.

Gwamnatin Sokoto na son ganin bayan ƴan ta'adda

A cewar sanarwar, haɗin gwiwar aikin jami'an tsaro da gwamnatin jihar ta ɗauki nauyinsa a yankin ya samu nasarori sosai.

An bayyana cewa nasarorin da jami'an tsaron suke samu sun ƙara dagula lamurran ƴan ta’addan da ke yankin waɗanda suka shiga halin ƙaƙani-kayi.

A yayin samamen an gano maboyar ƴan ta’adda da dama tare da lalata su, yayin da aka kashe wasu daga cikinsu.

Hakazalika, jami'an tsaron sun ceto ɗaruruwan mutanen da aka yi garkuwa da su a yayin wannan aiki da suke ci gaba da gudanarwa.

Wace tunatarwa gwamnatin ta yi?

Sanarwar ta yi kira ga mazauna yankin su kasance masu lura tare da sanar da hukumomi duk wani motsi da basu yarda da shi ba a yankunansu.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan tankar mai ta sake fashewa a Najeriya, mutane 11 sun rasu

"Ƴayin da jami’an tsaro ke ƙara matsa lamba kan ƴan ta’adda, suna tserewa zuwa wasu yankuna tare da waɗanda suka samu raunuka daga cikin su."
"Muna wayar da kan jama’a don jawo hankalinsu kan su yi taka tsantsan, saboda wasu daga cikin ƴan ta’addan na iya yin basaja domin neman mafaka a ƙauyuka ko neman a duba lafiyarsu a asibitocin karkara."

- Kanal Ahmed Usman

Gwamnati ta ƙarfafa gwiwar mazauna yankunan kan su riƙa kai rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi ba ga hukumomin tsaro.

Ta bayyana cewa yin hakan zai tabbatar da tsaron jihar da inganta tattalin arziƙinta, bisa tsarin manufofin Gwamna Ahmed Aliyu guda tara.

Ƴan ta'addan Lakurawa sun kashe sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na sojoji sun rasa ransu bayan sun yi artabu da ƴan ta'addan Lakurawa a ƙaramar hukumar gudu ta jihar Sokoto.

Sojoji biyar ne suka rasa ransu yayin da aka kashe ƴan ta'adda mutum shida bayan an ɗauki dogon lokaci ana musayar wuta a tsakanin ɓangarorin biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng