Ana Neman Raba Ministan Wuta da Mukaminsa, An Fadi Gazawarsa ga Tinubu da Duniya

Ana Neman Raba Ministan Wuta da Mukaminsa, An Fadi Gazawarsa ga Tinubu da Duniya

  • Kungiyar Kwadagon Najeriya (NLC) ta nemi Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya yi murabus saboda ci gaba da rushewar tushen wuta
  • Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya zargi ma’aikatar da gazawa wajen rashin fifita gyaran cibiyoyin wutar lantarki a kan ayyuka marasa amfani
  • Kungiyar ta yi gargadi cewa idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba, za a ci gaba da fuskantar matsalolin da ke kara ragewa jama’a kwarin gwiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta nuna bacin ranta kan halin da bangaren wutar lantarki na kasar ya tsinci kansa.

NLC ta bayyana cewa bangaren wutar lantarki na fuskantar barazanar durkushewa gaba daya fadin kasar nan.

Ministan wuta
NLC ta bukaci ministan lantarki ya yi murabus. Hoto: Bayo Adelabu|Kola Onanuga
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya zargi ministan lantarki, Adebayo Adelabu da rashin iya sauke nauyin da ke kansa.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Joe Ajaero ya ce yawan rushewar tushen wutar lantarki a karkashin mulkin ministan ya ninka duk abin da aka taba gani a tarihin kasar nan.

NLC ta jefi ministan wuta da gazawa

A cewar Joe Ajaero, ma’aikatar wutar lantarki tana fuskantar rashin shugabanci nagari, wanda ya sa tushen wutar lantarki ke ci gaba da rushewa ba tare da daukar matakan gyara ba.

Joe Ajaero ya ce;

“Idan da ma’aikatar tana hannun kwararru, da an dakile wannan abin kunya na yawaitar rushewar tushen wutar lantarki.
Wani bayani maras tushe daga ministan yana cewa wannan matsala za ta ci gaba kamar dai ta zamo dabi'a.”

Shugaban NLC ya bayyana hakan a matsayin tabbataccen shaidar gazawar ma’aikatar, inda ya nemi ministan ya yi murabus domin bada dama ga wanda zai iya ayyukan cikin kwarewa.

Shugabannin NLC da TUC yayin wani taro a 2024. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Ana neman korar ministan wuta da ya ware Naira biliyan 8 wayar da kan 'yan kasa
Asali: Twitter

Batun kashe N8bn don wayar da kai

NLC ta kuma soki shirin kashe Naira biliyan 8 da aka sanya a kasafin kudin 2025 domin wayar da kan jama’a kan biyan kudin wutar lantarki, tana mai cewa wannan shiri ba shi da amfani.

Kara karanta wannan

"Ana saye ra'ayin 'yan adawa da N50m": Atiku ya tona asirin gwamnatin Tinubu

A cewar shugaban kwadago;

“Lokacin da 'yan kwangila ke bin TCN bashin sama da Naira biliyan 200, yin amfani da Naira biliyan 8 domin koyar da jama’a yadda za su biya kudin wuta ya zama abin dariya.”

Zargin rashin kwarewa a hukumar NERC

Kungiyar ta kuma zargi Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) da rashin iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Shugaban NLC ya bayar da misali, inda ya ce NERC ta hada kai da wani kamfanin rarraba wutar lantarki domin sallamar shugaban kamfanin saboda rashin gaskiya.

Joe Ajaero ya ce:

“Wannan yana nuna cewa NERC ba ta shirya sauke nauyin da ke kanta ba, saboda haka dole ne a yi gyara a cikin hukumar.”

Kungiyar NLC ta gargadi gwamnati

A karshe, NLC ta yi gargadi ga gwamnatin tarayya cewa rashin daukar matakin gyara zai kara dagula lamura a bangaren wutar lantarki da kuma rage kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su

Ajaero ya ce;

“Muna nan tsaye domin ganin cewa duk wanda ya gaza, an dauki matakin ladabtarwa a kansa, kuma ba za mu lamunci almubazzaranci da kudin jama’a ba.”

Kungiyar ta yi kira da a sanya fifiko kan gyaran cibiyoyin wutar lantarki domin kaucewa durkushewar bangaren gaba daya.

Dalilin kara kudin katin waya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin kara kudin katin waya, aika sakonni da data da kashi 50% a Najeriya.

Ministan sadarwa da tattalin yanar gizo ya bayyana cewa dole ce ta saka gwamnati kara kudin saboda matsalolin tashin farashin kayayyaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng