Sojojin Najeriya Sun Yi Fatattaka, Sun Aika Dakarun Turji 7 zuwa Barzahu

Sojojin Najeriya Sun Yi Fatattaka, Sun Aika Dakarun Turji 7 zuwa Barzahu

  • Dakarun Operation fansan yamma sun kashe manyan mayakan Bello Turji bakwai, ciki har da Abu Dan Shehu da Jabbi Dogo
  • An kai samame maboyar 'yan ta'adda da ke jihar Sakkwato, inda aka shafe tsawon lokaci ana rugugin wuta a kan 'yan bindiga
  • An lalata sansanonin Turji a Shinkafi da Isa, tare da kwace makamai, babura, da sauran kayan aiki da ake amfani da su wajen kai hari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Dakarun Operation fansan yamma sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 24, ciki har da manyan shugabanni bakwai na Bello Turji.

Sojojin sun gudanar da aikin da ya share mayakan daga doron kasa a cikin mako guda, ta hanyar kutsawa maboyar da yawa daga cikin 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Turji
Sojoji sun hallaka dakarun Turji Hoto: Nigerian Army HQ
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa dakarun sun samu nasarar aiki ne da hadin gwiwa tsakanin Dakarun Musamman na Rundunar Sojojin Najeriya 1 Brigade da Sojojin Ruwa na Musamman.

An gudanar da wannan aiki a kauyen Gebe, karamar hukumar Isa, Jihar Sakkwato, a ranar 22 Janairu, 2025 a kokarin kakkabe yan bindiga daga Arewacin Najeriya.

Dakarun Bello Turji da sojoji su ka kashe

An gano cewa bayanan sirri sun kai samamen da ya lalata cibiyoyin Turji a yankunan Shinkafi da Isa, inda aka samu nasarar kashe manyan mayakan dan ta'addan.

Daga cikin mayakan da aka kashe akwai; Abu Dan Shehu, Jabbi Dogo, Dan Kane, Basiru Yellow, Kabiru Gebe, Bello Buba, Dan Inna Kahon Saniya da aka fi sani da Ya fi Bahaushe.

Yadda sojoji su ka ragargaji 'yan ta'adda

Sojoji sun kai hare-haren sama tare da kai hare-haren bazata kan sansanin 'yan ta'adda da ya lalata maobyar migayun tare da hallaka da yawa da cikinsu.

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

Zaratan dakarun sun yi nasarar kwace makamai, alburusai, da babura da 'yan bindigan su ke amfani da su wajen tada zaune tsaye a cikin al'umma.

Sojoji sun yi nasara a kan 'yan ta'adda

Dakarun Turji da aka kashe suna taka muhimmiyar rawa wajen tsara hare-hare da samar da makamai a kungiyar da ta addabi jama'a.

Wannan kisa da aka yi wa dakarun zai kawo babban nakasu a kan shirin da Bello Turji ya ke yi wajen kai hare-hare kamar yadda ya saba a baya.

Dakarun Sojoji sun matsawa 'yan ta'adda

Sojojin Najeriya sun ƙara matsa lamba kan ‘yan ta’adda a watannin baya-bayan nan, sakamakon ƙaruwar hare-hare, sace-sace, da kisan kai a Zamfara, Sakkwato, Katsina, da Kebbi.

Bayan sun rike wutar, sun yi nasarar kashe shugabannin Turji bakwai, rushe sansanonin 'yan bindiga.

Sojoji na zargin Turji ya tsere

A wani labarin, mun ruwaito cewa ana zargin shugaban 'yan bindiga, Bello Turji ya tsere daga mahaifar tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, bayan hare-haren sojoji domin ya tsira.

A ranar 19 da 20 Janairu, an ga mabiyan Turji suna hijira tare da raunuka a kan babura daga Maradun zuwa wuraren Garsa/Kadanya bayan sojojin sun kashe dan fitinannen dan ta'addan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng