Bikin Kur'ani: Malami Ya Jefewa Izala da Darika Kalubale kan Tara Alarammomi a Abuja
- Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana shakkunsa kan taron Qur’anic Festival da za a gudanar karkashin jagorancin Sarkin Musulmi a Abuja
- Malaman Izala da Darika sun bayyana cewa za su halarci taron, wanda za a tara mahaddatan Qur’ani har 30,000 daga sassan Najeriya
- Wani alaramma a jihar Yobe ya bayyana wa Legit matakin da zai dauka a kan taron da ake shirin gudanarwa a watan gobe a Abuja
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Majalisar Kolin Addinin Musulunci ta Najeriya ta shirya babban taron da aka kira Qur’anic Festival, wanda za a gudanar a Abuja tare da mahalarta daga sassa daban-daban.
An ruwaito cewa Malaman Izala da Darika za su halarci taron domin nuna goyon baya, yayin da ake sa ran taron zai tara mahaddata Qur’ani har 30,000.

Asali: Facebook
A wani bidiyo da Abu Nauwwara Sidiq Ibrahim ya wallafa a Facebook, malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Barista Ishaq Adam Ishaq ya yi tsokaci kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi kira ga malamai su fayyace ko irin wannan taron yana da asali a cikin addinin Musulunci.
An nemi karin bayani kan Qur’anic Festival
Malamin ya bayyana cewa Kur’ani littafin Allah ne wanda aka saukar domin shiryar da mutane, ba domin biki ko taro ba.
Malamin ya ce;
“Addini shi ne Allah ya ce, Annabi ya ce, sahabbai sun ce. Idan ba haka ba, ya kamata malamai su yi mana bayanin halaccin irin wannan taro.”
Ya jaddada cewa duk wani abu da ake dangantawa da addini dole ne a tabbatar da cewa magabata sun yi shi, idan kuwa babu wannan tabbaci, to akwai bukatar a yi karin bayani.
Haka zalika, Sheikh Ishaq ya ce:
“Idan taron addini ne, dole a tabbatar sahabbai sun yi makamancinsa. Idan kuwa siyasa ce, bai kamata a yi amfani da Qur’ani domin siyasa ba,
"Domin hakan zai zama tamkar izgili da littafin Allah.”
Ka da a yi amfani da Kur’ani don siyasa
Malamin ya nuna damuwarsa kan yiwuwar amfani da Qur’ani wajen cimma manufofin siyasa, yana mai cewa hakan bai dace ba.
“Idan siyasa ce, bai kamata a yi wasa da Qur’ani ba. Amma idan ka je wurin, abin da aka raba ka karba, ka bar musu siyasarsu,”
- Sheikh Ishaq Adam Ishaq
Shawarar Ishaq Adam ga mahaddatan Kur’ani
Sheikh Ishaq ya ce duk mai halartar taron ya kamata ya san me ake nufi da taron. Ya yi kira ga mahalartan da cewa:
“Idan abin addini ne, sai ka je ka yi. Amma idan siyasa ce, bai kamata ka bari a yi amfani da Qur’ani wajen siyasa ba.”
Ya kara jan hankali kan mahimmancin koyon karatu, fahimtar ma’anar Qur’ani, da kuma aiki da shi.
Malamin ya ce an saukar da Kur'ani ne domin:
- Imani da shi
- Karatunsa
- Sanin ma'anarsa
- Aiki da shi
Taron Qur’anic Festival ya haifar da muhawara tsakanin malamai da jama’a, inda wasu ke goyon bayan taron yayin da wasu ke ganin akwai bukatar karin bayani kan halaccinsa.
Legit ta tattauna da alaramma
Wani mahaddacin Kur'ani a jihar Yobe, Kale Abubakar ya bayyanawa Legit cewa har yanzu akwai bukatar karin haske a kan taron.
"Idan ya tabbata ba gwamnati ba ce ta shirya taron, zan halarta matukar an bude kofar gayyata. Domin ina jin tsoron kada 'yan siyasa su yi amfani da mu,"
- Kale Abubakar
An soki taron makaranta Kur'ani
A wani rahoton, kun ji cewa an soki malaman addini a Najeriya kan shirin shirya taron makaranta Kur'ani a birnin tarayya Abuja.
Farfesa Usman Yusuf na cikin wadanda suka yi magana kan taron yayin da wasu 'yan Najeriya suke zargin akwai siyasa a lamarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng