Madalla: 'Yar Kano da dan Zamfara sun lashe musabakar Al-Kur'ani ta mata da maza

Madalla: 'Yar Kano da dan Zamfara sun lashe musabakar Al-Kur'ani ta mata da maza

- A yau Asabar, 27 ga watan Maris ne aka rufe taron gasar karatun Al-Kur'ani mai girma ta kasa wanda aka yi jihar Kano

- Wani hazikin dalibi mai suna Muhammad Auwal Gusau wanda ya fito daga jihar Zamfara ne yayi nasarar lashe gasar ta maza kuma a matakin izu 60

- Har ila yau Nusaiba Shuaibu Ahmad, yar asalin jihar Kano ce ta zo ta daya a matakin izu 60 na mata

Rahotanni sun kawo cewa an kammala gasar karatun Al-kur'ani mai girma ta kasa a jihar Kano a yau Asabar, 27 ga watan Maris.

An fara gasar karatun littafin mai tsarki ne kwanaki takwas da suka gabata, inda aka kammala shi a cikin kwana ta tara, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

A bangaren gasar ta maza, Muhammad Auwal Gusau wanda ya fito daga jihar Zamfara ne yayi nasarar lashe gasar.

Madalla: 'Yar Kano da dan Zamfara sun lashe musabakar Al-Kur'ani ta mata da maza
Madalla: 'Yar Kano da dan Zamfara sun lashe musabakar Al-Kur'ani ta mata da maza Hoto: BBC
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: 2023: Dalilin da yasa muka bari tsohon Shugaban hafsan soji ya dawo cikinmu, APC ta magantu

Ya kara da masu karatu da dama samman a karshe ya samu nasara a matakin karatun izu 60 da tafsiri.

Sannan a bangaren mata kuma, Nusaiba Shuaibu Ahmad, yar asalin jihar Kano ce ta zo ta daya a matakin izu 60.

A wajen taron an nadawa Muhammad Auwal Gusau rawani, cewa ya zama zakaran gwajin dafi a tsakanin gwanayen al-Kur'ani mai girma.

Manyan makaranta daga sassa daban-daban na kasar sun halarci taron wanda ya samu halartan sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Haka kuma mafi yawan wadanda ba su samu nasara ba tun daga matakin farko na gasar har zuwa karshe sun halarci taron rufe gasar.

KU KARANTA KUMA: Babu dan siyasa na hakika da zai yi watsi da damar zama shugaban kasa – Fayemi

A wani labari na daban, mahaifin daya daga cikin daliban makarantar FCFM Afaka 39 da yan bindigan suka sace a jihar Kaduna, Ibrahim Shamaki, ya mutu.

Channels TV ta rahoto cewa Ibrahim, mahaifi ne ga Fatima Shamaki, daya daga cikin dalibai matan da suka bayyana a bidiyon da yan bindigan suka saki.

A cewar majiya daga iyalan mamacin, Ibrahim Shamaki ya mutu sakamakon bugun zuciya bayan rashin lafiyan da ya fada bayan samun labarin sace diyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel