Abba Ya Kwace Filayen da Ganduje Ya Raba, za a Karasa Ayyukan Kwankwaso a Kano

Abba Ya Kwace Filayen da Ganduje Ya Raba, za a Karasa Ayyukan Kwankwaso a Kano

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin farfado da ayyukan tashar manyan motoci da aka yi watsi da su a Dakatsalle da Gundutse
  • Ayyukan sun fara ne a zamanin mulkin Rabiu Musa Kwankwaso a 2014, amma an bar su a lokacin da Abdullahi Umar Ganduje ya karbi mulki
  • A cewar gwamnatin Kano, matakin da Abba Yusuf ya dauka zai rage cunkoso, kara tsaro a kan hanyoyi, da bunkasa tattalin arziki a jihar Kano

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana aniyarsa ta farfado da ayyukan tashoshin manyan motoci a yankin Kano ta Kudu.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, bayan wata ziyarar ba-zata da gwamnan ya kai wurin aikin da aka bari a Dakatsalle.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Abba Kabir
Abba Kabir Yusuf zai karasa aikin da Kwankwaso ya fara. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa|Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

Legit ta tattaro maganganun da Abba Kabir Yusuf ya yi ne a cikin wani sako da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar gwamnatin Kano, an fara ayyukan ne a zamanin mulkin Rabiu Musa Kwankwaso, amma aka bar su a lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.

Ayyukan da aka bari a Kano tun 2014

An fara tashoshin manyan motocin Dakatsalle, Gundutse, da Dawanau ne a 2014 karkashin gwamnatin Kwankwaso, amma sun tsaya cik a mulkin Abdullahi Ganduje.

Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan yadda motocin dakon kaya ke haifar da cunkoso a cikin birnin Kano, wanda ke kawo cikas kan zirga-zirgar jama’a da tattalin arziki.

Ya kuma ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala ayyukan Dakatsalle da Gundutse domin tabbatar da tsaro da saukaka zirga-zirga.

Gwamna Abba Gida Gida ya soki watsi da ayyukan

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida ya jawo hadimin Kwankwaso, ya nada shi a Mukami

Gwamnan ya bayyana cewa watsi da aikin tashar manyan motoci a Dawanau tare da baiwa mutane filayen wurin aikin ba tare da bin ka’ida ba, abu ne mara kyau.

Ya bayyana hakan a matsayin cin amanar jama’a, yana mai cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci irin wannan hali ba.

"Idan aka farfado da wadannan tashoshin, ba kawai za su saukaka cunkoso ba ne, za su kuma samar da dama ta tattalin arziki ga jama’a,"

- Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Kano ta kwace filaye

Sanusi Bature ya ce gwamnan ya umarci hukumomin da suka dace da su tabbatar da dabbaka dokokin hanyoyi domin ganin babu wata hanya da aka toshe saboda taruka ko wasu dalilai.

Gwamnatin jihar ta kuma soke raba fili da aka yi a wuraren aikin tashar Dakatsalle da Gundutse domin ba wa aikin damar cigaba.

Bayan kammala ayyukan, za a mika tashoshin ga Kungiyar Masu Motocin Hanya ta Kasa (NARTO) domin tafiyar da su yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Gwamnan ya yi alkawarin cewa wannan matakin zai inganta hanyoyi, rage cunkoso, da bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Abba ya yi aiki a mahaifar Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da karasa aikin hanya a mahaifar magabacinsa, Dr. Abdullahi Ganduje.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya gaza karasa aikin ne a lokacin da yake gwamnan jihar duk da cewa a mahaifarsa ta ke.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel