"Sarakuna na da Rawar da Za Su Taka," Sanusi II Ya Caccaki Masu Auren Mata 4 babu Hali

"Sarakuna na da Rawar da Za Su Taka," Sanusi II Ya Caccaki Masu Auren Mata 4 babu Hali

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya taɓo batun aure da haihuwa barkatai ba tare da mallakar abin da zai ɗauki nauyinsu ba
  • Sanusi II ya ce sarakuna za su taka muhimmiyar rawa wajem magance waɗannan kalubale musamman mutuwar mata masu juna biyu
  • Mai martaba ya shawarci mutane da su rika yin tsarin iyali da tallafawa mata domin inganta harkokin kiwon lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a yi amfani da tsarin gargajiya wajen magance ƙalubalen zamantakewar al'umma.

Mai martaba sarkin ya ce ta hanyar amfani da tsarin, za a iya kawo ƙarshen cin kashin da ake wa matan aure da mace-macen masu juna biyu a cikin al'umma.

Sarki Muhammadu Sanusi II.
Muhammadu Sanusi II ya nuna damuwa kan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, ya ba da shawari Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Sanusi II ya yi wannan furuci ne a taron cibiyar al'umma da kiwon lafiya watau ACEPHAP wanda aka shirya a jami'ar Bayero da ke Kano, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarakuna za su taka muhimmiyar rawa

Basaraken ya jaddada muhimmancin wayar da kan al'umma kai tsaye ta hanyar tsarin usuli watau sarakunan gargajiya domin su ke kusa da jama'a.

“Ci gaban al’umma bai kamata ya tsaya kan abin da gwamnati ta ke yi kawai ba; sai an shigo da matakan gunduma, kauye da yankuna, inda ake samun sarakunan gargajiya”

- Muhammadu Sanusi II

Ya yi nuni da cewa dole ne a fifita kula da mata da yara, yana mai cewa matsalar mutuwar mata masu ciki da jarirai tana da alaka da sakaci.

A cewar Sarki Sanusi II, ana iya rage wannan matsaloli na mutuwar mata masu juna biyu da jarirai ta hanyar daukar matakan kulawa da samar da abinci mai kyau.

Mai martaba ya ba da shawarar amfani da bayanai wajen bibiyar ciki da haihuwa a lokaci guda, domin bai wa sarakunan gargajiya damar daukar matakan kariya.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki

Sanusi II ya soki yawan aure da haihuwa

Ya kuma soki al'adu da tunanin al'umma da suka hada da haihuwa barkatai ba tare da isassun kuɗin ɗaukar nauyin iyali ba.

Muhammadu Sanusi II ya ce wannan tunanin na mutane da ke sa su riƙa haihuwa barkatai na kara jawo tabarbarewar kiwon lafiyar al'umma.

“Mutum wanda ba zai iya kula da mace ɗaya ba shi za ka ga ya auri mata huɗu rigis, kuma ya haifo yara 15, sannan ba zai iya ba ɗaukar nauyin kula da lafiya da iliminsu ba."
"Wannan yana haifar da rashin wadatar abinci mai gina jiki da nauyin da al'umma ba za ta iya dauka ba,” in ji shi.

Sarkin Kano ya ba al'umma mafita

Sarkin Kano ya ƙara da yin kira ga al’umma da su rungumi tsarin iyali, ilimi da tallafawa mata domin inganta harkokin lafiya.

Sanusi ya buƙaci haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, cibiyoyin ilimi, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin ƙasashen duniya don samar da tsare-tsare masu dorewa a bangaren lafiya.

Kara karanta wannan

China na gina kamfanin $200m a Nasarawa, za a biya ma'aikata N500,000

Sanusi II ya sake magana kan manufofin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Muhammadu Sanusi ya yi ƙarin haske kan kalaman da ya yi game da manufofin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sarkin ya bayyana cewa an yi masa gurguwar fahimta, abin da mutane ke yaɗawa ba haka yake nufi ba kwata-kwata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel