"Malamanmu Sun Yi Kuskure," An Fara Raddi ga Shirin Taron Kur'ani a Abuja

"Malamanmu Sun Yi Kuskure," An Fara Raddi ga Shirin Taron Kur'ani a Abuja

  • Farfesa Usman Yusuf ya yi zargin cewa wasu malamai daga bangaren Izala sun yi amfani da addini wajen yaudarar talakawa
  • Ana zargin za a kashe Naira biliyan biyu kowace rana don gudanar da addu’o’i a Abuja, abin da ya jawo suka daga al’ummar Arewa
  • Farfesa Yusuf, dattijo a Arewa ya bayyana cewa wasa da addini shi ne ya kawo matsalolin tsaro kamar Boko Haram da ISWAP

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Taron mahaddata Al Kur’ani 60,000 ya fara jawo ce-ce-ku-ce, musamman daga Arewacin Najeriya, yayin da ake shirin tattara malaman Musulunci a Abuja.

An ruwaito cewa ana shirin kashe akalla Naira biliyan biyu a kullum domin gudanar da addu’o’i ga kasa gabanin azumin watan Ramadana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Abdullahi Bala Lau
An zargi malaman sunna da bidi'a Hoto: Abdullahi Bala Lau/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Farfesa Usman Yusuf, daya daga cikin dattijan Arewacin kasar nan a hirarsa da DCL ya bayyana takaicinsa bayan ya zargi malaman da cin amanar talakawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zargi malaman Sunnah da bullo da sabuwar bidi’a a addinin musulunci, irin wacce aka saba gani a wajen Kiristocin Kudancin kasar nan.

An zargi malaman Sunnah da yaudarar talakawa

Farfesa Usman Yusuf ya zargi malaman da shigewa gaba wajen yaudarar ‘yan Najeriya su zabi shugaban Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Ya bayyana cewa kamata ya yi Malaman su shiga dakunansu, su dage da istigfari saboda irin azabar da su ka taimaka aka jefa jama'a a ciki.

Farfesa Yusuf ya ce:

“Balle wannan bangaren na Izala su ka zo su ka marawa shugaban Bola Ahmed Tinubu baya, ya na neman zabe, malaman da mu ke kira malaman Muslim-Muslim, aka zo aka yaudari jama’a cewa ga muslim-muslim, shugaban kasa da mataimakin shi, in su ka zo za su taimaki musulunci. Cikin kuri’u miliyan takwas, miliyan biyar na Arewa ne.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

An zargi malaman Izala da ci da addini

Farfesa Usman Yusuf ya zargi malaman sunnah da karbar kwangilar yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kamfe domin sake neman kujerar shugaban kasa a 2027.

Ya bayyana takaicin yadda malaman za su jefa rayuwar mahaddata Al-Kur'ani daga jihohin Arewa da ke fama da rashin tsaro domin biyan bukatar kashin kai.

"Tashin hankalin shi ne, matsalolin da ke faruwa a Arewa, daga Mai tatsine ne, har Boko haram, har 'yan ISWAP, har Ansarudden da Darussalam, wasa da addini ne ya kawo wannan."
"Wasa da addini shi ne an zo an yi amfani da addini, an yaudari mutane sun yi zabe, kuma an zo ana gallaza masu azaba.

Ya shawarci malaman da su daina amfani da addini ana zaluntar talakawa, tare da zarginsu da karbo sabuwar kwaniglar tallata Tinubu a 2027.

Malami ya yi addu'a a kan shugabancin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya yi addu'ar Allah watsa duk wani yunkuri da shiri da ake yi wajen sake zabar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Haba Malam': Hadimin Tinubu ya zargi El Rufa'i da neman rusa gwamnati kan sukar APC

Ya bayyana haka ne ta cikin wani faifan bidiyo da ya fitar, ya yi addu'ar Allah Ya kawo sauki a lamarin Najeriya da ya sake damalmalewa tun bayan saukar Muhammadu Buhari daga mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.