Tinubu: Yadda Gwamnatina Ta Daure Mutane Sama da 100 Masu Daukar Nauyin Ta'addanci

Tinubu: Yadda Gwamnatina Ta Daure Mutane Sama da 100 Masu Daukar Nauyin Ta'addanci

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta samu nasarar yanke hukunci a kan masu ɗaukar nauyin ta’addanci
  • Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta dakile kudade da kayan tallafin da ke bai wa Boko Haram da ISWAP damar kai hare-hare
  • Shugaban kasar ya yi alkawarin cewa za a ci gaba da daukar dukkanin matakan da su ka dace wajen kawo karshen ta'addanci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ofishin mai ba shi shawara a kan (ONSA) da haɗin gwiwar Ministan Shari’a da Antoni-Janar na Tarayya ya haifar da da mai ido.

Shugaban ya bayyana cewa hadin kai tsakanin ofisoshin biyu ya samar da nasarar gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci a gaban kotu, an kuma yanke masu hukunci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

Tinubu
Gwamnati ta ce ana kokarin kawar da talauci Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Guardian ta wallafa cewa ce Tinubu ya fadi hakan ne a Abuja yayin taron kasa a kan dakile halasta kudin haram, yaki da ta’addanci da NFIU ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, kotu ta samu nasarar yanke hukunci kan fiye da mutane 100 da aka samu da hannu a tallafawa ta’addanci cikin shekaru biyu da suka gabata.

Yadda gwamnatin Tinubu ke yakar ta’addanci

This day ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta bullo da hanyoyin sanya idanu a kan rashin tsaro da kokarin magance ta’addanci a duniya.

Tinubu, wanda Sakatare na Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya wakilta, ya ce gwamnati na daukar matakan wajen shawo kan matsalar ta’addanci.

Ya ce:

“Mun dakile kudade da kayan tallafin da ke bai wa Boko Haram da ISWAP damar ci gaba da kai hare-hare kan al’umma. Wannan mataki zai bai wa yankunan karkara damar sake farfadowa.”

Tinubu: An samu nasarorin yakar ta’addanci

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Shugaban kasar nan ya yi nuni da cewa hadin gwiwar da ake samu tsakanin ‘yan sanda, EFCC, ICPC da NDLEA na samar da nasara a yaki da ake yi da ta’addanci.

Shugaban ya kara da cewa:

“Ayyukan binciken sun karkata ne kan kungiyoyin da ke shirya waɗannan laifukan, tare da manufar rushe dukkan cibiyoyin da ke tallafa musu.”

Tinubu ya jaddada cewa gwamnatin sa na ƙoƙarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya, tare da tabbatar da cewa an rage tasirin ta’addanci da ta’asa a cikin al’umma.

Ana zargin malamai da yi wa Tinubu kamfe

A wani labarin kuma, kun ji yadda wani dattijo a Arewacin Najeriya ya zargi malaman Izala da sake karbo kwangila daga fadar shugaban kasa domin tallata Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.

Wannan ya biyo shirin taron addu'a da malaman su ka shirya, inda za a gayyaci mahaddata Al'Kur'ani domin su hallara a babban birnin tarayya, za a shafe mako guda ana karatun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.