Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dalilin Kara Kudin Katin Waya Ana Shirin Kai Ta Kotu

Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dalilin Kara Kudin Katin Waya Ana Shirin Kai Ta Kotu

  • Ministan sadarwa da tattalin yanar gio, Bosun Tijani ya kare karin kudin katin waya sadarwa yayin da gwamnati ke fuskantar barazanar shari’a
  • Bosun Tijani ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan aiki da tsadar shigo da kayayyaki daga ketare ne suka jawo karin kudin waya, sako da data
  • Kungiyar SERAP da NATCOMS sun yi barazanar kai gwamnatin tarayya kotu domin neman a janye karin kudin da suka ce ba bisa ka’ida yake ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin yanar gizo, Bosun Tijani ya kare karin kudin katin waya da data na kashi 50% duk da rashin jin dadin da jama’a ke nunawa.

Ministan ya bayyana hakan ne a gaban ‘yan majalisa yayin da yake kare kasafin kudin ma’aikatarsa, inda ya ce lamarin ya zama dole lura da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Bola Tinubu
Gwamnatin Najeriya ta fadi dalilin kara kudin katin waya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Rahotan Punch ya nuna cewa kungiyoyi kamar NATCOMS da SERAP sun yi barazanar kai gwamnati da hukumar NCC kotu idan ba a janye karin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karin kudin waya a Najeriya

Ministan sadarwa ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a duniya da tsadar gudanar da ayyukan sadarwa sun sa dole a kara kudin.

“Yawancin abubuwan da mutane ba sa lura da su shi ne cewa, mun bar kamfanoni masu zaman kansu su dauki nauyin saka hannun jari a harkar sadarwa."
"Wadannan kamfanoni suna saka jari ne kawai a wuraren da za su iya samun riba,”

- Bosun Tijani

A bisa dukkan alamu ministan ya yi jawabin ne domin gamsar da 'yan kasa, musamman masu shirin kai gwamnati kara kotu game da karin kudin.

Bosun Tijani
Ministan sadarwan Najeriya, Bosun Tijani yayin wani taro. Hoto: Federal Ministry of Information and Digital Economy
Asali: Twitter

Barazanar maka gwamnatin Tinubu a kotu

Kungiyar NATCOMS ta ce za ta yi kokarin ganin NCC ta janye karin kudin ta hanyar tattaunawa, amma idan hakan bai yi tasiri ba, za su maka gwamnati da hukumar a kotu.

Kara karanta wannan

China na gina kamfanin $200m a Nasarawa, za a biya ma'aikata N500,000

Shugaban NATCOMS, Adeolu Ogunbanjo ya bayyana cewa kungiyar za ta amince da karin kashi 5% zuwa 10%, amma ba kashi 50% ba.

Ita kuwa SERAP ta bayar da wa’adin sa'o'i 48 ga gwamnati da kamfanonin sadarwa su janye karin kudin.

Vanguard ta wallafa cewa kungiyar SERAP ta ce:

“Idan ba a janye wannan karin da ba bisa ka’ida ba, za mu hadu a kotu,”

Tasirin karin kudin kan 'yan kasa

Karin kudin taro ya jawo ce-ce-ku-ce daga 'yan kasa da kuma kungiyoyi da ke kare hakkin jama’a.

Jama’a na ganin cewa wannan karin zai fi shafar masu karamin karfi da ke amfani da sadarwa wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Hukumar NCC ta bayyana cewa ta amince da wannan kari ne saboda tsadar gudanar da ayyukan sadarwa, duk da cewa kamfanonin sadarwa sun nemi karin kashi 100%.

Duk da kukan da jama'a ke yi, gwamnatin tarayya ta na ganin ta tausaya wajen yarda da karin kashi 50% maimakon kashi 100%.

Kara karanta wannan

Malamin da ya je Nijar ya ce sojoji sun tsananta tsaro, ya gargadi 'yan Najeriya

An shawarci Tinubu kan hulda da Donald Trump

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan Najeriya ya gargadi shugaba Bola Tinubu kan fito na fito da Donald Trump na Amurka.

Farfesa Bolaji Akinyemi ya ce ya kamata Bola Tinubu ya rika kawar da kai ko da Trump ya nemi su yi musayar yawu kan abubuwan da suka shafi Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng