'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Manyan Malamai a jihar Kogi, Suna Neman N20m

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Manyan Malamai a jihar Kogi, Suna Neman N20m

  • Masu garkuwa da mutane sun sace fastoci uku a Ejule, jihar Kogi, bayan wa’azi inda suke neman Naira miliyan 20 kudin fansa
  • Daya daga cikin wadanda aka sace, Evang. Gabriel Onaji, tsohon fasto ne a Ejule kuma an tsinci motarsu a daidai inda aka sace su
  • Rundunar ‘yan sanda ba ta bayar da cikakken bayani kan satar ba, yayin da mazauna garin ke rokon gwamnati ta ceto fastocin uku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace fastoci uku a Ejule, karamar hukumar Ofu ta jihar Kogi bayan wa'azi.

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun tare fastocin a kan titin Ejule-Ofakaga-Anyigba da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Litinin, 20 ga Janairu.

An shiga fargaba a Kogi yayin da 'yan bindiga suka sace wasu fastoci masu wa'azi
'Yan bindiga suna neman a biya su N20m da suka yi garkuwa da malaman addini a Kogi. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun sace fastoci uku a Kogi

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Daga cikin fastocin akwai Evang Gabriel Onaji, wanda ya kasance bakon mai wa'azi a taron kwanaki uku da aka gudanar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Evang Sunday Oguche, wanda ya shirya wa’azin, ya tsallake rijiya da baya saboda ya shiga garin Anyigba, maimakon Ejule, inda aka yi garkuwa da fastocin.

Fastocin sun bar wajen da aka kammala taron wa'azin a rana ta biyu, inda suke kan hanyarsu ta komawa masaukinsu lokacin da aka tare su.

Bayanin malaman addinin da aka sace

Rahoto ya nuna cewa an tsinci motar malaman addinin a gefe da hanya a Ofakaga, kusa da hanyar Ejule-Anyigba.

Masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansa har Naira miliyan 20 kafin su saki fastocin, inji wani mazaunin Ejule mai suna Ayefu John.

Evang Gabriel Onaji yana daga cikin wadanda aka sace, kuma shi ne tsohon faston Coci na United Evangelical Church (UEC) a Ejule.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Har yanzu ba a gano sunayen sauran fastocin biyu da aka sace ba, amma ana zargin su ne mataimakan Evang Sunday Oguche.

Al'ummar Ejule sun roki a ceto fastocin

'Yan garin sun tabbatar cewa fastocin da aka sace suna cikin tawagar Evang. Oguche, wanda shi ne babban mai shirya wa'azin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin, kuma kakakin rundunar SP Williams Aya bai amsa waya ba.

Al’ummar Ejule sun bayyana damuwa kan tsaro a yanzu, tare da rokon gwamnati da hukumomi su hanzarta ceto fastocin da aka yi garkuwa da su.

'Yan bindiga sun sace malaman Adamawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa ‘yan sanda Adamawa sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da malaman cocin EYN biyu, Rabaran James Kwayang da Rabaran Ishaku Chiwar.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Suleiman Nguroje ya ce an sace limaman ne a Mbila-Malibu da misalin karfe 11 na dare a karamar hukumar Song.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

SP Suleiman Nguroje ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro don tabbatar da ceto malaman daga hannun masu garkuwa da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.