'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari a Borno, Sun Yi Gumurzu da Dakarun Sojoji
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai sabon hari a ƙauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno
- Tsagerun sun ƙona motocin jami'an tsaro tare da dasa ababen fashewa a harin da suka kai daga dajin Sambisa
- Dakarun sojoji sun samu nasarar daƙile harin ƴan ta'addan bayan an ɗauki dogon lokaci ana musayar wuta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Wasu ƴan ta'adda da ake zargin mambobin Boko Haram ne sun kai hari a ƙauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun ƙona motocin sintiri guda uku na 'yan rundunar CJTF da kuma tankunan yaƙi guda uku mallakar sojoji.

Asali: Twitter
Ƴan Boko Haram sun kai hari a Borno
Jaridar Vanguard ta ce wata majiya ta bayyana cewa harin ya tilastawa mazauna yankin guduwa cikin daji don tsira da rayukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma tattaro cewa sojoji sun fafata da ƴan ta'addan amma ba a samu asarar rai ba.
Sai dai, abin takaici, ƴan ta'addan sun dasa abubuwan fashewa a kan hanyar Konduga-Kawuri don hana isowar ƙarin sojoji daga Konduga.
Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin da aka turo sun yi nasarar shiga Kawuri, amma wani mamban CJTF, Abba Godori, ya taka bam ɗin da aka dasa, inda ya rasa ransa nan take a safiyar ranar Talata.
Sojoji sun daƙile harin Boko Haram
Zagazola Makama ya bayyana cewa dakarun sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar daƙile harin da ƴan ta'adda suka kai a Kawuri, daga dajin Sambisa a safiyar Talata.
Majiyoyi sun bayyana cewa artabun wanda ya ɗauki kusan awa biyu, ya zo ƙarshe ne bayan ƴan ta'addan sun janye sakamakon asarar da suka samu daga ɓangarensu.
Majiyar ta ƙara da cewa ƙarin sojojin da aka turo sun fuskanci kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa tallafawa abokan aikinsu, amma sun yi nasarar fatattakar ƴan ta'addan.
Kwamanda ya yabawa sojoji
A wani mataki na nuna goyon baya, kwamandan runduna ta musamman ta 21 ya ziyarci sojojin bayan fafatawar, inda ya yaba da jarumtarsu tare da kira gare su da su ci gaba da jajircewa a ayyukansu.
Kwamandan ya kuma ziyarci iyalan wanda ya rasa ransa sakamakon bam ɗin da ƴan ta’addan suka dasa yayin harin.
Ya tabbatar musu da samun goyon bayan sojoji yayin da ya jaddada buƙatar ci gaba da ƙarfafa gwiwar jami'an tsaron.
"Ba a gama wannan yaƙi ba. Dole ne ku kasance cikin shirin ko ta kwana."
- Kwamandan sojoji
Sojoji sun kashe shugaban ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wani hatsabibin shugaban ƴan bindiga, Na Ballo, a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun kashe Na Ballo wanda na hannun daman Ado Aliero ne yayin wani zazzafan artabu da suka yi a ƙaramar hukumar Tsafe.
Na Ballo ya daɗe yana ayyukan ta'addanci a Gabashin Takulawa da ke cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng