Talaka Zai Ji a Jikinsa: NNPCL Ya Kara Kudin Man Fetur, An Sanar da Sabon Farashi

Talaka Zai Ji a Jikinsa: NNPCL Ya Kara Kudin Man Fetur, An Sanar da Sabon Farashi

  • Kamfanin NNPC ya kara farashin man fetur zuwa N990 a Abuja da N965 a Lagos, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a
  • Wannan na zuwa ne kwanakin kadan bayan gidan mai a fadin kasar sun kara farashin man fetur zuwa tsakanin N1,050 da N1,150
  • A hannu daya kuma, hukumar NMDPRA ta bayar da lasisin gina sabuwar matatar mai mai karfin ganga 10,000 ga MRO Energy a Delta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin NNPCL ya kara farashin man fetur a gidajen mansa a jiya Tala, abin da ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a.

Farashin fetur a gidajen man NNPCL ya tashi daga N965 zuwa N990 a Abuja, yayin da a Lagos aka kara shi daga N925 zuwa N965.

Kamfanin NNPCL ya kara kudin man fetur a Legas da Abuja
Kamfanin NNPCL ya kara kudin man fetur a gidajen mansa na Abuja da Legas. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

An kara kudin man fetur a Najeriya

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun sanar da saukar farashin fetur bayan karyewar abinci

Rahoton jaridar The Guardian ya nuna cewa an samu karin kudin ne biyo bayan sauye-sauyen kasuwa da kuma tsarin cire tallafin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan karin farashin ya zo ne kwanaki bayan da farashin litar fetur ya tashi zuwa tsakanin N1,050 da N1,150 a gidajen man kasar nan.

Matatar man Dangote da wasu masu rumbunan ajiyar mai sun kara farashin man fetur daga N899 zuwa N955 a tashoshin lodinsu.

Gidajen NNPCL sun fara amfani da sabon farashi

Hakan na faruwa ne saboda karin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, inda farashin Brent ya kai dala 81 a kan kowace ganga.

Masu sayar da mai sun yi gargadin cewa karin farashin danyen mai zai shafi fitar da mai a cikin gida, kuma zai kara farashin fetur a gidajen mai.

Rahotanni sun nuna cewa gidajen mai na NNPC da na manyan 'yan kasuwa sun fara amfani da sabon farashin man.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

Za a gina sabuwar matatar mai a Delta

A gefe guda, hukumar NMDPRA ta amince da bayar da lasisin gina sabuwar matatar mai a jihar Delta.

Hukumar ta bai wa kamfanin MRO Energy Limited damar gina matatar mai da za ta tace ganga 10,000 kowace rana a garin Imode da ke Ughelli.

Wannan matakin ya zo bayan watanni biyu da hukumar ta baiwa Process Design and Development Limited lasisin gina matata mai tace ganga 27,000 a Gombe.

A sakon da aka wallafa a shafin NMDPRA na X, Engr. Farouk Ahmed ya gabatar da lasisin matatar mai ga kamfanin MRO Energy Limited a Delta.

'Yan kwadago na adawa da kara kudin fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar NLC ta yi tir da karin farashin litar man fetur zuwa tsakanin N1,050 da N1,150, tana mai cewa matakin ya wuce kima.

NLC ta bayyana cewa karin farashin man zai kara wahala ga talakawa, yana shafar farashin abinci, sufuri, da hauhawar farashin kayayyaki.

Kara karanta wannan

Hajjin 2025: Gwamnati za ta ba alhazai kyautar kudi, an ji nawa maniyyaci zai samu

Farfesa Theophilus Ndubuaku ya ce gwamnati ba ta tuntubi masu ruwa da tsaki ba kafin daukar matakan da ke shafar rayuwar al’umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.