Yadda Gwamnoni Suka Sauya Kudirin Harajin Tinubu, Ya Dace da Bukatunsu

Yadda Gwamnoni Suka Sauya Kudirin Harajin Tinubu, Ya Dace da Bukatunsu

An kai ruwa rana tsakanin shugabannin Arewa, musamman gwamnoni da gwamnatin tarayya kan kudirin haraji kafin su samu daidaito bayan sauye sauye

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tun a lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudirin haraji a majalisar dokoki lamarin ya fara jan hankalin 'yan Najeriya.

Kudirin ya samu kakkausar suka daga 'yan Najeriya musamman daga yankin Arewa kafin daga baya a samu daidaito tsakanin gwamnoni da gwamnatin tarayya.

Gwamnoni
Abubuwan da gwamnoni suka zaftare a kudirin harajin Tinubu kafin yarda da shi
Asali: Twitter

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu abubuwa da gwamnonin Najeriya suka sauya a kudirin kafin su amince da shi a makon da ya wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da suka jawo rudani a kudirin haraji

Abubuwa uku (3) ne suka fi jan hankali da jawo kai ruwa rana tsakanin gwamnoni da gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

1. Raba harajin VAT

Abubuwan da aka buga muhawara a kansu a cikin kudurin harajai da aka gabatarwa Majalisar Ƙasa sun haɗa da shawarar raba kashi 60 na harajin VAT bisa kokarin jihohi na tara haraji.

Daily Trust ta wallafa cewa hakan na nufin jihohi za su karɓi kuɗi gwargwadon adadin harajin VAT ɗin da aka samar a yankunansu.

Rahoton Punch ya nuna cewa batun ya zama babbar matsala tsakanin gwamnonin jihohi da 'yan majalisa, musamman daga Arewacin ƙasar nan.

2. Karin kudin VAT

Wata matsalar da aka buga a kanta ita ce ƙarin kuɗin VAT, wanda kudirin harajin Bola Tinubu suka tanada domin ƙara adadin harajin daga lokaci zuwa lokaci.

A karkashin kudirin, za a kara harajin daga kashi 7.5% zuwa kashi 10% a shekarar 2025, kashi 12.5% a 2026, sannan a ci gaba da ƙarin haraji har ya kai kashi 15% zuwa shekarar 2030.

Kara karanta wannan

Kungiya ta gano sabuwar matsala a rabon harajin VAT, an gargadi gwamnonin Najeriya

Bayan sukar gwamnoni, lamarin ya sha suka daga wasu 'yan kasa inda suke cewa za samu karin kudin kayayyaki idan lamarin ya tabbata kamar yadda Tribune ta rahoto.

3. Zare kudin NASENI, TETFUND da NITDA

Matsala ta uku ita ce, kudirin ya nuna cewa harajin da aka ware domin tallafawa hukumomi kamar NASENI, TETFUND, da NITDA za a dakatar da su nan da shekarar 2030.

Duk da haka, wadannan hukumomi za su ci gaba da samun tallafi daga kasafin kuɗi domin tabbatar da ayyukansu na ci gaba da inganci.

Wannan ma ya sha suka daga gwamnoni da kungiyar malaman jami'a ta ASUU inda suka ce lamarin ba zai yi kyau ga harkar ilimi ba.

Abubuwan da gwamnoni suka sauya

Kungiyar gwamnonin Najeriya da kwamitin gyaran haraji na shugaban kasa, sun haɗu a ranar 16 ga Janairu, 2025, domin tattauna muhimman batutuwan ƙasa.

Kara karanta wannan

Zaman kotu ya gamu da tangarɗa da yan bindiga suka kai hari, an kashe fitaccen lauya

Gwamnoni
Gwamnoni da 'yan kwamitin kudin haraji bayan tattaunawa a Abuja. Hoto: Nigeria Governors Forum
Asali: Facebook

Cikin abubuwan da suka tattauna akwai gyaran manufofin kuɗi da tsarin harajin Najeriya, kuma sun cimma waɗannan matsayoyi:

1. Sauya yanayin raba harajin VAT

Ƙungiyar ta sauya yadda za a rika raba harajin VAT ga jihohi a domin tabbatar da daidaiton raba albarkatun kasa a kan:

  • Kashi 50% bisa raba daidai
  • Kashi 30% bisa kudin da jiha ta samar
  • Kashi 20% bisa yawan jama’a

Sabon kason kudin ya saba yanayin rabon harajin da shugaba Bola Tinubu ya gabatar a cikin kudirin harajin kamar yadda Daily Trust ta wallafa a Facebook.

A tsarin shugaban kasa, za a raba wa jihohi kaso 60% na abin da suka samo na haraji yayin da gwamnonin suka mayar da shi kashi 30%.

2. Dakatar da kara harajin VAT

Gwamnonin sun amince cewa ba za a ƙara yawan kuɗin VAT ba ko rage harajin kuɗin kamfanoni (CIT) a wannan lokacin domin kiyaye daidaiton tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Mahdi Shehu ya shiga matsala a hannun DSS, an maka shi a kotu kan zargin ta'addanci

Ƙungiyar ta ba da shawarar ci gaba da cire harajin kayayyakin noma daga VAT domin tattabar da jin daɗin al’umma da ƙarfafa samar da amfanin gona.

Wannan ma ya ci karo da bukatar shugaban kasa ta cewa za a cigaba da kara harajin VAT har ya kai zuwa kashi 15% a 2030.

3. Soke dakatar da kudin TETFUND, NITDA

Taron gwamnoni ya ba da shawarar cewa ba za a saka sharadin kawo karshen kudin da ake samarwa TETFUND, NASENI da NITDA ba.

Wannan ma ya saba bukatar shugaba Tinubu a cikin kudirin inda ya bukaci a dawo da su cikin kasafin kudin kasa maimakon tara musu kudi ta haraji.

A karshe, kungiyar gwamnoni ta nanata cikakken goyon bayanta ga gyaran tsarin dokokin harajin Najeriya da suka tsufa bisa sharadin da ta ambata.

Tinubu zai raba kudi ga talakawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya za ta fara raba kudin ga 'yan Najeriya domin rage musu radadin rayuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu: Yadda Gwamnatina ta daure mutane sama da 100 masu daukar nauyin ta'addanci

Gwamnatin Bola Tinubu za ta raba kudi har N75,000 ga kimanin mutabe miliyan 70 domin rage musu radadin tsadar rayuwa da talauci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng