'Yan Bindiga Sun Dira Babbar Kasuwa a Yobe, Sun Kashe Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Dira Babbar Kasuwa a Yobe, Sun Kashe Bayin Allah

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi dirar mikiya a kasuwar Ngalda da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe
  • Ƴan bindigan sun kashe mutane bakwai tare da raunata wasu mutum 11 a yayin harin wanda suka kai da yammacin ranar Litinin
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce jami'anta sun cafke shugaban waɗanda ake zargi da kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Ƴan bindiga sun hallaka mutum bakwai waɗanda yawancinsu ƴan kasuwa ne a jihar Yobe.

Ƴan bindigan sun kuma raunata wasu mutum 11 a harin da suka kai kasuwar dabbobi da ke Ngalda, ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe.

'Yan bindiga sun kai hari a Yobe
'Yan bindiga sun kai hari a kasuwar jihar Yobe Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai hari a kasuwar Yobe

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a kasuwar ta mako-mako da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi tare da yin fashi a shaguna.

Kara karanta wannan

'Yan sa kai sun yi ta'asa a Neja, 'yan sanda sun yi caraf da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauda Yakubu Damazai, mai taimakawa shugaban ƙaramar hukumar Fika a ɓangaren kafofin sadarwa, ya bayyana cewa mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a harin da ƴan bindigan suka kai.

"A yammacin jiya (Litinin), wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a babbar kasuwa da ta dabbobi da ke Ngalda. Sun kashe mutane bakwai da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba."
"Aƙalla mutane 11 sun samu raunuka kuma an garzaya da su zuwa asibitin Fika don samun kulawar likita. Alhamdulillah, jami’an tsaro da ƴan sa-kai sun kashe uku daga cikin ƴan ta'addan."
"Shugaban ƙaramar hukumar Fika, Hon Audu Bukar Gadaka, ya kai ziyarar ta'aziyya, inda ya roƙi Allah Ya gafartawa waɗanda suka rasa rayukansu, Ya kawo sauƙi ga mutanen da ke kwance a asibiti."

- Dauda Yakubu Damazai

Ƴan sanda sun ɗauki mataki

Jami'in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da aukuwar lamarin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

Kakakin ƴan sandan ya ce harin wata tawagar ƴan fashi ta mutum shida, karkashin jagorancin Datti Alhaji Dadji daga garin Ngalda suka kai shi.

Ya ce harin ya yi sanadiyyar rasa rayuka bakwai da raunuta wasu mutane 11, yayin da ƴan fashin suka tafi da kuɗaɗe da suka kai kimanin naira miliyan 16.5.

"A yayin maida martani, mutanen garin Ngalda sun haɗa kai inda suka kashe uku daga cikin ƴan fashin, yayin da sauran uku suka tsere da raunuka."
"DPO na ƴan sanda ya jagoranci tawagar sintiri zuwa gidan Datti Alhaji Dadji, inda suka gano wata bindiga ƙirar gida tare da harsasai guda uku."
"An cafke Datti Alhaji Dadji wanda yanzu haka yake tsare a hannun ƴan sanda yana fuskantar tambayoyi yayin da ake ci gaba da bincike."

- SP Dungus Abdulkarim

Ƴan bindiga sun kori mutane a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa hare-haren ƴan bindiga sun tilastawa mutanen Kauru da ke jihar Kaduna tserewa daga gidajensu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

Shugaban raya al'ummar ƙaramar hukumar Kauru, ya bayyana sama da mutane 500 sun yi hijira daga gidajensu yayin da wasu da dama suka rasa rayukansu, sakamakon hare-haren ƴan bindigan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng